Mutum 7 sun mutu a wani hargitsi da yan sa kai a kasuwar Dankolo jihar Kebbi


Bayan yan bindiga sun kai farmaki a kauyen Ayu wanda ke karkashin Bena a Masarautar Wasagu kwana uku da suka gabata, lamari da ya sa wasu yan sa kai suka je kasuwar Dan kolo bisa zargin cewa sun san wasu daga cikin wadanda suka yi aika aika a kauyen Ayu, kuma suna kyautata zaton za su same su a kasuwar Dankolo.

Sakamakon haka washe gari ranar Lahadi 1 ga watan Satumba suka je kasuwar Dankolo, lamari da ya karkare ga haddasa mutuwan wasu mutane  cike har da Fulani.

Sai dai bincike da muka gudanar ya nuna cewa babu wanda ya tura su aikata wannan aiki a cikin kasuwar Dankolo. Lamari da ya ci karo da kokarin da Gwamnatin jihar Kebbi ke ta yi domin ganin an tsabtace tsarin tafiyar da ayyukan yan sa kai wanda ya hada da hana daukan doka a hannu ta hanyar kashe rai na wanda ake zargi da aikata laifi nan take.

Kazalika, wata majiya da ke da masaniya kan harkar tsaro a jihar Kebbi da bata son a ambaci sunanta, ta shaida mana cewa an umarci yan sa kai idan har za su je wajen irin wannan aiki na taimaka wa kai, su tabbata cewa sun je tare da jami'an tsaro. Majiyar ta ce a wannan lamari na Dankolo, yan sa kai sun je ne bisa rabin kansu.

Kazalika, wata majiya ta shaida mana cewa, an tabbatar da ganin gawa bakwai da aka kashe a wannan hargitsi na garin Dankolo, kuma akwai wasu mutum hudu da suka sami raunuka.

Sai dai har ya zuwa yanzu, hukumar yansandan jihar Kebbi bata fitar da bayani kan lamarin ba, wata majiya ta shaida mana cewa hukumar na ci gaba da tattara bayanai da bincike kan lamarin a matakin yanzu.

Sakamakon bincike da muka gudanar, ya nuna cewa shugaban yan sa kai na Masarautar Zuru, Mr.John Mani, baya da masaniyar shiga kasuwar Dankolo da wasu yan sa kai suka yi. Sai dai yanzu haka suna gudanar da bincike na hadin gwiwa tsakaninsa da Kwamandan shiya na yansanda yankin Zuru,da jami'in DSS domin warware ainihin yadda lamarin ya faru, bisa numarnin manya kan harkar tsaro na Gwamnatin jihar Kebbi.. 

Yayin da ake yawan zargin wasu Fulani da aikata aika aika da suka hada da sace shanaye, fashi da makami, dauke mutune domin karbar kudimin karbar kudin fansa da sauransu a Masarautar Zuru.

Kazlika ana zargin yan sa kai, wacce wasu matasa suka ba da lokacinsu domin fuskantar kowane bata gari da ke aikata wadannan aika aika a Masarautar da wuce wuri wajen aikata aikinsu, duk da yake suna jefa rayukansu cikin hatsari, amma ana zarginsu da kashe rayuka da basu ji basu gani ba, ko aikata ba daidai ba. 

Mun samo cewa Gwamnatin jihar Kebbi tana kokari wajen sake fasalin yadda yan sa kai ke gudanar da aikinsu a Masarautar Zuru. Tare da sanar da sabuwar dokar ababebe da ya kamata su kauce wa aikatawa lokacin da suke gudanar da ayyukan sa kai, da ya shafi tsaro.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN