Kotu ta daure yaya da ƙanwa saboda satar naira miliyan 1.7 a Kaduna


Wata babban kotu a Jihar Kaduna, a ranar Talata, ta yankewa wasu mata biyu yaya da ƙanwa (Maryam da Rukaiya) hukuncin gidan yari an shekaru 10 saboda satar naira miliyan 1.7 kamar yadda The Punch ta ruwaito.

An gano cewar ƴan uwan biyun da suka mallaki gidauniyar Jamal Health Foundation sunyi amfani da shafinsu na dandalin sada zumunta don neman tallafin kuɗi na taimakawa mara lafiya a 2019.

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa ƴan uwan sun karkatar da kuɗaɗen da suka samu daga hannun ƴan Najeriya sunyi hidimomin gabansu.

Hukumar Yaƙi da Rashawa ta EFCC, cikin sanarwar da Shugaban Sashin Hulda da Jama'ar ta, Wilson Uwujaren, ya fitar ya ce ɗaya daga cikin wanda suka bada tallafi, Badamasi Shanon ya yi ƙorafi kan matan biyu cewa ba suyi amfani da kuɗin don dalilin da suka karba ba.

Wani sashi na cikin sanarwar ta ce, "Wani Alhaji Badamasi Shanono a ƙorafin da ya shigar a 2019 ya yi zargin cewa Gidauniyar Jamal Health Foundation mallakar ƴan uwan biyu ta hanyar amfani da dandalin sada zumunta ta nemi tallafin kuɗi don yi wa wani Usman Umar magani sakamakon rashin lafiya da ke fama da ita na tsawon shekaru biyu.

"Shanono ya yi ikirarin cewa ya bawa gidauniyar tallafin naira miliyan ɗaya yayinda wata mata ta bada N700,000. Ya ƙara da cewa Jamal Health Foundation ta ƙi bawa mara lafiyar kuɗin sai dai ta yi amfani da kuɗaɗen don wasu buƙatun kanta."

Mai Shari'a Muhammad Tukur ya yanke wa ƴan uwan biyu hukuncin zaman gidan yari na shekaru 10 da zaɓin tarar naira 100,000 bayan sun amsa laifinsu kan tuhumar cin amana.

A wata sanarwa ranar Juma'a, mai taimakawa gwamnan ɓangaren yada labarai, Mukhtar Gidado, ya ƙaryata zargin cewa uban gidansa na cikin jerin gwamnoni da zasu koma jam'iyya mai mulki.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.

Source: legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN