Hargitsi ya barke tsakanin jami'an hana fasa kwabri NCS da wasu yan smugal a garin Igbo-Ora da ke jihar Oyo, sakamakon haka mutum 3 suka mutu cikinsu har da wani Laftana na soji mai suna Lt. Josia Peter.
Yayin tabbatar da lamarin, Kakakin hukumar yansandan jihar Oyo SP Olugbemiga Fadeyi, ya ce hargitsin ya faru ne tsakanin jami'an Kwastam na Federal Operations Unit (FOU), Zone A da wasu yan smogal ranar Juma'a 20 ga watan Nuwamba.
Ya ce yansanda na gudanar da bincike kan musabbabin aukuwan lamarin da ya kai ga mutuwan Laftana na soji tare da mutum 2 sakamakon raunukan harsashi da suka samu.
DAGA ISYAKU.COM
https://chat.whatsapp.com/
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari