Gwamnatin jihar Kaduna ta dakatad da Wazirin Zazzau saboda adawa da Sarki


Gwamnatin jihar Kaduna ta dakatad da shugaban kwamitin masu zaben sarkin Zazzau, Wazirin Zazzau, Alhaji Ibrahim Aminu, Sahara Reporters ta ruwaito.

Hakazalika ta gargadi Iyan Zazzau, Aminu da sauran mambobin kwamitin zaben sarkin uku su canza lauyansu zuwa lauyan gwamnati a karar da suka shigar kotu, kan nadin Ahmed Nuhu Bamalli a matsayin sabon Sarkin Zazzau.

Za ku tuna cewa Iyan Zazzau, ya shigar da kara kotu inda ya ke kalubalantar nadin Ahmad Bamalli matsayin sabon sarkin masarautar.

Gwamnatin jihar, a wasikar da sakataren din-din-din na ma'aikatar harkokin kananan hukumomi ya rattafa hannu a madadin kwamishanan, ta sanar da dakatad da Wazirin Zazzau.

"Mun fahimci cewa sabon sarkin da gwamnatin jihar sun yiwa masu zaben sarki barazanar su canza lauyansu zuwa lauyan jihar, saboda su rattafa hannu kan jawabin rantsuwa," wata majiya ta bayyanawa Sahara Reporters.

"Barazanar da Sarki da gwamnatin jihar keyi ne ya sa aka aika wasikar tuhumar ranar 12 ga Nuwamba, 2020."

"Kawo yanzu dai, daya daga cikin masu zaben sarkin ya amince da canza lauyansa zuwa na gwamnati."

Mu kawo muku cewa an aikewa 'yan majalisar sarki takardar tuhuma mai taken "rashin halartar taron tattaunawa da ma'aikatar kananan hukumomi ta shirya"

Daga cikin wandanda aka aikewa takardar akwai limamin Zazzau, Wazirin Zazzau, Limamin Kona da Makama Karami kan rashin halartar wani taro da aka yi kan shirin bikin mika sandar sarauta ga sabon sarkin Zazzau.

An bada awa 48 ga wanda suka karbi tuhumar da suyi bayani, sai dai wani rahoto ya nuna wasu daga cikin masu zaben sarkin, basa jin dadin yadda al'amura ke gudana a masarautar.

Source: Legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN