Auren tagwaye a Kano: 'Burimmu mu haifi tagwaye su auri tagwaye kamar mu'


Ɗan shekara 33 Hassan Sulaiman Indabawa da Hussaininsa za su auri tagwaye Hassana da Hussaina Ado Ashir a Kano da ke arewacin Najeriya.

Za a daura auren tagwayen ne a ranar Lahadi 22 ga watan Nuwamba a garin Kano.

Sun shaida wa BBC cewa burinsu shi ne su haifi tagwaye, su ma su yi auren tagwaye.

Hassan ya ce tun lokacin da suke ƙanana, suna yin abubuwa iri ɗaya da shi da Hussaininsa, kuma tsarinsu shi ne su auri tagwaye.

"Tun muna yara, muna yin komi tare, muna saka tufafa iri ɗaya, mu ci abinci tare, kuma kullum aji ɗaya muke a makaranta. A makarantar koyon aikin jinya da muka kammala lambarsa ita ce 010, tawa kuma 011."

"Da daɗewa, burinmu shi ne mu auri tagwaye, kuma ko danginmu suna faɗa muna mu auri tagwaye, kafin yanzu mun sha gwada sa'armu da wasu tagwayen amma abubuwa su kasa daidaita kamar yadda muke so, amma yanzu muna cikin farin ciki domin mun cimma burinmu," a cewar Hassan.

Di twins for dia pre-wedding shoot

Hassan wanda shi ne yaya, ya ce sun haɗu da amarensu su ne ta hanyar wani abokin yayansu wanda ya haɗa su da tagwayen.

"Wata uku bayan haɗa mu, ba mu gansu ba, duk lokacin da muka je gidansu ba su nan har sai wata rana Allah Ya sa muka haɗu kuma komi ya tafi daidai, sun kasance kamar mu sun tashi tare komi nasu tare."

Matarsa Hassana ta shaida wa BBC cewa tana cikin farin ciki yadda ita da ƴar uwarta suka auri tagwaye.

Di twin grooms

"Babu kalmar da za ta iya bayyana irin farin cikin da nake ji a yanzu. Ina jin cewa addu'ar da mutane ke yi cewa Allah Ya sa mu auri tagwaye shi ne ya faru."

Hussaini ya ce haɗin kai yana da muhimmanci a gare su, sun kuma ce abin da ya faru da wasu fitattun mawaƙa ba abin daɗi ba ne.

"Haɗin kai matsayinku na tagwaye yana da muhimmanci kamar yadda muka ga abin da ya faru da mawaƙa su P square waɗanda tagwaye ne kamar mu ba ma jin daɗin, wannan wani ƙarfafa guiwa ne da muka dage kan tagwaye kamar mu su dinga yin abubuwa tare."

Hassana and Hussaina

Daga ƙarshe matarsa Hussaina ta ce tsawon shekaru 23 da suke duniya ita da ƴar uwarta ba su taɓa yin wani abu ba tare ba, don haka wannan muhimmin lokaci ne a gare su.

"Ko da yaushe muna tare, tun daga firamare har zuwa yanzu da muke karatu a kwalejin ilimi, muna bacci da ɗaki ɗaya, gado ɗaya, amma yanzu wannan zai sauya," a cewarta tana murmushi.

Source: bbc


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN