Abubuwa 4 da ka iya sa Donald Trump shan kaye a zaben Amurkan yau Talata


Bayan kimanin shekaru hudu a ofis a matsayin shugaban kasar Amurka, Donlad Trump, na bukatan yan kasar su sake zabensa karo na biyu a zaben dake gudana yau.

Babban abokin hamayyarsa a zaben da ke gudana yanzu haka shine dan takaran jam'iyyar Democrat, Joe Biden.

Legit.ng ta zakulo muku wasu kura-kurai da ka iya sabbabawa Donald Trump shan kaye a zaben:

1. Siyasantar da annobar Coronavirus

Salon da shugaba Trump ya dauka wajen yaki da cutar Korona na iya zama babban dalilin da ya sa wasu ba zasu zabeshi ba.

Misali, lokacin da shugabannin kasashen duniya ke daukan matakai masu tsauri domin dakile cutar, Trump ya siyasantar da lamarin kuma yayi mata rikon sakainar kashi.

A bisa binciken Pew, shugaba Trump ya yi jinkiri wajen daukan mataki.

Kawo yanzu mutane 230,000 suka rasa rayukansu sakamakon cutar, Worldometer ta ruwaito.

2. Kalaman wariyar launin fata

Shugaba Trump ya shahara wajen kalamai dake ishara zuwa ga wariyar launin fata kuma bakaken fara musamman na iya zaben abokin hamayyarsa, Biden.

3. Saba alkawari

Akwai wasu alkawuran zabe masu muhimmanci ta Trump bai cika ba har yanzu kuma hakan na iya zama matsala.

Daga cikin alkawuran shine gina bango tsakanin Amurka da Mexico wanda har yau ya gaza.

Hakazalika ya yi alkawarin soke tsarin Obamacare kuma ya maye gurbinta da sabon tsari. Ya soke ta amma bai maye gurbinta da wani tsarin ba.

4. Yaki da yan gudun hijra

Sabbin ka'idojin yan gudun hijra da Trump ya samar zai isa sa mazauna kasar wadanda ba yan asali bane watsi da shugaban kasan.

Tun lokacin da ya hau mulki, Trump ya haramtawa wasu yan kasashe shiga Amurka gaba daya. Yawancin kasashen Larabawa ne.

Bayan haka ya fara raba iyaye da yaransu saboda iyayen ba yan Amurka bane amma sun haifi yaran a Amurka.

Mun kawo muku cewa a tarihin Amurka, shugabannin kasa suna samun nasarar tazarce bayan karewar wa'adinsu na farko saboda irin ayyukan da suka yi.

Amma ba haka ake gani tattare da Donald Trump ba saboda lokacin da ya kaddamar yakin neman zabensa a 2019, maki 43% kadai ya samu, cewar Gallup.

Business Insider ya bayyana cewa tun daga lokacin makin ke cigaba da sauka.

Source: Legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN