2023: Ba za mu iya cewa ga yankin da magajin Buhari zai fito ba - Buni


Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta bayyana cewa ba ta yanke shawara kan yankin da za ta mika wa tikitin Shugaban kasa ba a 2023. Shugaban kwamitin rikon kwarya na jam’iyyar ta kasa, Gwamna Mai Mala Bunin a jihar Yobe, ya bayyana hakan a lokacin wata hira da jaridar Saturday Sun.

Legit.ng ta fahimci cewa tattaunawa kan wanda zai karbi shugabanci daga hannun Shugaban kasa Muhammadu Buhari a 2023 na kara daukar dumi Manyan yan siyasa da suka hada da tsohon gwamnan jihar Lagas Bola Tinubu, Gwamna Ahmad El-Rufai na Kaduna, Sanata Orji Uzor Kalu, da sauransu sun samu goyon baya domin karbar mulki daga hannun Buhari.

Hukumar zabe ta asa mai zaman kanta (INEC) ta sanar da cewar za a yi zaben Shugaban kasa na gaba a ranar 28 ga watan Fabrairun 2023. Yayinda ake ta tambaya kan inda APC za ta mika tikitin Shugaban kasarta bayan wa’adin Buhari/Arewa, Gwamna Buni ya ce jam’iyyar mai mulki na sake gina kanta tare da sasanta fusatattun mambobinta.

Ya bayyana cewa kwanan ne jam’iyyar ta tsallake rijiya da baya sakamakon rikicin shugabanci wanda ya yi sanadiyar tunkude shugabancin Adams Oshiomhole “Ba za mu iya cewa ga inda ciyaman ko Shugaban kasa na jam’iyyar zai fito ba. Ba za mu iya tsallake gada ba har sai mun kai wajen.

“A halin da ake ciki, kwamitin na aikin sake gina jam’iyyar ne ta yadda za ta iya jure duk wani abu a wannan lokaci da kuma ci gaba da kasance jam’iyya mai mulki a Najeriya." A gefe guda, Kungiyar Nasiriyya a jihohi 21 sun bayyana aniyarsu ta janyo gwamnan Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya tsaya takarar shugaban kasa a babben Zaben 2023.

Source: Legit

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN