Yanzu yanzu: Yadda aka gwabza fada tsakanin Hausawa da Yarbawa a Iju-Ishaga


Ana rikici yanzu haka tsakanin Hausawa da Yarabawa a Fagba, Iju-Ishaga, karamar hukumar Ifako-Ijaye inda aka kona gidajen mutane kuma hankulan mazauna sun tashi, cewar Vanguard. Har yanzu babu jami'an tsaron da suka je kuma ba'a adadin wadanda abin ya shafa ba tukun.

Kakakin hukumar yan sanda jihar, ya tabbatar da hakan kuma ya yi kira ga shugabannin garin su yiwa matasans magana. Ya ce ita kanta hukumar yan sandan na fuskantar matsala. "Akwai dokar hana fita kuma kowa ya koma gida. Aiki ya yiwa yan sanda yawa, mu hada kai domin kawo karshen lamarin," Kakakin yace. Daya daga mazauna yankin, Aina, ya bayyanawa The Punch cewa "Mun kasa fita daga gudajenmu.

Tun ranar Talata suka fara fada. Mun yi tunanin abin ya tsaya jiya ne amma suka cigaba yau." "Ban san abinda ya janyo fadan ba, kawai na ga mutane na ta guje-guje." A bangare guda, mai bada shawara na musamman ga shugaban kasa kan kafar watsa labarai, Femi Adesina ya ce wasu masallatai da coci-coci da wasu kafafen baza labarai na kiyayya. Ya kara da cewa zanga zangar EndSARS wata dama ce da wasu suke amfani da ita don watsa sakonnin kiyayya kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Source: Legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN