Sabon tsarin albashin 'yan sanda na zuwa nan babu dadewa - Buhari


Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana sabon salon biyan albashin jami'an 'yan sanda, inda ya umarci hukumar albashi ta kasa da tayi gaggawar amsar canjin. Shugaba Buhari ya fadi hakanne a jawabin kai tsaye a ranar Alhamis da yamma.

Buhari yace, "Don tabbatar da jindadi da walwalar 'yan sanda, an umarci hukumar albashi da tayi gaggawar tabbatar da sabon tsarin albashin jami'an 'yan sandan. Ana duba a kan yadda za'a bullo wa albashin sauran jami'an tsaro."

A wani labari na daban, Sifeta janar na 'yan sandan Najeriya IGP Mohammed Adamu, ya bada umarnin janye dukkan 'yan sandan da ke tsaron lafiyar manyan mutane a fadin kasar nan. Kamar yadda aka gano, wannan hukuncin ya biyo bayan bukatar sake assasa dokar dakile zanga-zangar EndSARS a tituna.

Wannan umarnin na kunshe ne a wani sako da aka mika ga dukkan kwamandojin 'yan sandan kasar nan a ranar Litinin wanda jaridar The Cable ta gani. A umarnin, wanda zai fara aiki a take, gidajen gwamnati, shugaban majalisar dattawa da kuma kakakin majalisar wakilai ne aka tsame.

"Sifeta janar na 'yan sandan Najeriya ya bada umarnin janye dukkan 'yan sandan da ke tsaron manyan mutane banda na gidajen gwamnati, shugaban majalisar dattawa da kakakin majalisar wakilai," sakon yace. An umarci dukkan 'yan sanda masu tsaron da aka janye da su gaggauta zuwa gaban kwamandansu.

Source: Legit



Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN