Kotun daukaka kara ta soke daukan Kuratan yansanda 10,000 da Safeto Janar na yansandan Najeriya Muhammed Adamu ya yi a 2019.
A hukunci da Kotun ta bayar da gagarumin rinjaye daga Alkalan Kotun ranar Laraba 20 ga watan Satumba, ta ce hukumar kula da harkokin yansanda Police Service Commission (PSC) ne kadai ke da hurumin daukan yansandan.
Kazalika Kotun ta dage cewa Safeto Janar na yansandan Najeriya IGP, baya da hurumin daukan yansanda aiki. Sakamakon haka, Kotun ta yi fatali da wani hukunci da wata babban Kotun tarayya ta yanke a Abuja ranar 2 ga watan Disamba 2019, inda ta ce IGP yana da hurumin daukan yansanda aiki.
https://chat.whatsapp.com/
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/