KAI TSAYE: Buhari ya kammala gabatar da kasafin kudin, ya fita daga majalisa


Komai ya kankama domin gabatar da kasafin kudin 2021 a gaban yan majalisar wakilai da na dattawa a hade. Buhari ya shiga zauren majalisar misalin karfe 11:07 na safe kuma aka mike tsaye domin taken Najeriya.

Sannan shugaban majalisar dattawa ya yiwa shugaba Buhari maraba kuma ya umurci Sanata Tolu Olubiyi yayi addu'an Kiristoci kuma dan majalisa Maliki yayi na Musulmai. 

11:22 AM 

Shugaban majalisar dattawa, Ahmed Lawan, yana gabatar da jawabinsa Ya yi magana kan illan da cutar Korona ta yiwa tattalin arzikin Najeriya da kuma irin hadin kai da kyakyyawan fahimtan dake tsakanin su da fadar shugaban kasa.

11:28 AM

Shugaba Buhari ya fara gabatar da jawabinsa ga yan majalisa

Ya jaddada niyyar tsamo yan Najeriya milyan 100 daga talauci cikin shekaru 10 masu zuwa. Ya ce gwamnatinsa zata dauki matasa 774,000 na ba da dadewa ba.

11:38 AM

Jawabin Buhari

"Za mu kammala ginin gadar saman 2nd Niger kafin karewar wa'adinmu. Za mu kaddamar da Titin Legas zuwa Ibadan nan ba da dadewa ba." Buhari "Zamu yaki yan bindiga, masu garkuwa da mutane da yan tada kura, " Buhari

11:40 AM

Buhari ya yiwa sabon Kasafi mai kasafin kudin farfado da tattalin arziki da hakuri) Mun yi kiyasin wannan kasafin kudin bisa wadannan abubuwa:

1. Farashin danyen mai a $40 ga gangan
2. Zamu fitar da gangar mai 1.86 milyan kulli yaumin
3. Kudin canji N379 ga $1 4. GDP 3%, hauhawa kuma 11.95% Cewar Buhari 11:49 AM Jawabin Buhari.... "Zamu karbo sabon bashin
4.82tr a shekarar 2021, " Buhari

12:38 PM Buhari ya gama jawabinsa, ya ajiye daftarin kasafin kudin kuma ya fita daga zauren majalisa Shugaba Muhammadu Buhari ya fita daga majalisa bayan kammala gabatar da kasafin kudin 2021 .

Source: Legit.ng


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN