Gwamnatin Kano ta ba masu sakin finafinai a YouTube wata 3 su yi rajista da hukuma


HUKUMAR Tace Finafinai da Ɗab'i na Jihar Kano ta yi kira da kakkausar  murya ga masu shirya finafinan Hausa masu dogon zango (series) da su ke ɗorawa a YouTube da su gaggauta zuwa su yi rajista da hukumar.
 
Shugaban hukumar, Alhaji Isma'ila Na'abba (Afakallah), shi ne ya yi wannan kiran ne a lokacin da ya ke tattaunwa da mujallar Fim a ofishin sa. 
 
Afakallah ya ce hukumar sa na da hurumin tace finafinan Hausa da ake saki a YouTube.
 
Ya yi nuni da cewa dokar hukumar ta tanadar da cewa mutum ba zai saki fim ta ko wace hanyar da kimiyya da fasaha ta zo da ita ba sai ya kai hukumar an tace shi kafin ya shigar da shi cikin al'umma, "in dai za ka sake shi a Jihar Kano kuma mutane su gani."
 
Kazalika shugaban ya faɗa wa mujallar Fim cewa, "Duk waɗanda su ke da mu'amala da Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano dole su kawo mana mu tace, saboda fim ɗin ana sakin sa a gari kuma masu turawa a waya, wato 'yan 'downloading', su na 'downloading' ɗin sa su na sakar wa mutanen mu su na kalla."
 
Ya bayyana cewa wasu 'yan Kannywood mamallakan tashoshi a YouTube sun fara zuwa hukumar domin a tace finafinan nasu.
 
Shugaban ya ce su na tace fim ta hanyar sunan da mai shi ya ba fim ɗin, kuma duk lokacin da mai fim ɗin ya shirya fitar wani ɓangaren na fim ɗin, wato 'episode', dole sai ya kai shi an tace shi sannan ya saki kayan sa. "Wannan ita ce ƙa'idar da aka kafa, kuma an fara ganin cigaba," inji Afakallah.
 
Da Fim ta tambaye shi ko akwai wani taron wayar da kai da hukumar tasa ta gudanar kan al'amarin, ganin cewa yanzu ne hankalin mutane ya karkata zuwa YouTube, sai ya amsa da cewa, "Mun kirawo waɗanda su ke da mafi akasari a cikin harkar YouTube ɗin kuma yanzu mun shiga ma gaba ɗaya mun ga adadin su waye su ke amfani da Youtube ɗin nan, don haka kuma za mu kirawo kamfani bayan kamfani domin mu zo mu yi taro da su mu kuma sanar da su menene hurumin hukumar. 
 
"Kuma wannan abin ya samu haɗin kai da mu da ita kan ta Hukumar Tace Finafinai ta Ƙasa, su ma kuma su na ta ƙoƙarin ya za a yi a yi abin nan. 
 
"Daɗin daɗawa kuma, mun ba su daga wannan watan da mu ke ciki na Oktoba zuwa watan farko na sabuwar shekarar 2021, ga duk wanda ya ke da wani fim na YouTube to ya sani dole in za a fita yin aikin 'series' ɗin sai an nemi izinin hukumar. 
 
"Kamar yadda galiban ɗin finafinan nan a Kano ake ɗaukar su, don haka babu yadda za a yi ka ce za ka yi amfani da Jihar Kano ka kuma sakar mana wani abu da ba zai girmama mutanen Jihar Kano ba kamar yadda girmama mutanen Kano shi ne bin doka, domin kare addinin su, al'adun su da yanayin zamantakewar su don kada a kawo abubuwan da za su gurɓata tarbiyyar al'umma.”
 
Da ya ke bayani kan irin tanadin da su ka yi don yin wannan aiki, shugaban ya bayyana cewa hukumar ta samar da tsarin nan na aiki da ilimin komfuta da intanet, wato ICT, domin sanin abubuwan da ke faruwa.
 
Ya ce, "Tunda yanzu zamani ya canza ya koma yanar gizo, hukumar na sa ran fara gudanar da shirya wannan ICT ɗin na wannan hukumar domin  aikin binciken ƙwaƙwaf da kuma sa ido kan duk masu wannan shafi na YouTube na ganin irin abin da za su sa a shafukan nasu.
 
"Kuma nan gaba fim ɗin, idan har an kammala wannan aiki, ba sai mutum ya zo ba, kawai za a turo mana kuma mu yi 'censoring' mu gani. 
 
"Za kuma mu iya zama da mutum ga mu ga shi a lokacin da mu ke tacewar kuma ya na kallo, sannan kuma a gyara maka gyararrakin ka, ka gyara ka ƙara turo mana, mu tabbatar an yi gyaran, sannan mu ajiye shi a rumbun adana bayanan mu a matsayin gyararre kamar yadda duniya ta ci gaba."
 
Mujallar Fim ta tambayi Afakallah me zai ce kan batun masu shirya finafinai su saka a YouTube ba tare da tantancewar hukumar ba, wanda an sha yin gwagwarmaya da irin su a baya.
 
Sai ya ce: "Mu na nan mu na ta ƙoƙari, kuma mu na samun haɗin kai da su. Illa dole za ka samu wasu ba za su bi ba.
 
"To amma dai har kullum abin da wannan hukumar ke magana shi ne mu na yin wannan abin ne domin ya taimake mu, kuma zai taimaki ita kan ta sana'ar.
 
"Kuma duk wanda ya sa mana mutumin da bai da rajista, ba za mu buɗe fim ɗin sa ba. 
 
"Amma kuma duk wanda ya yi kunnen ƙashi, dole shi ma ya ga ba daidai ba; za mu ɗauki matakin doka a kan shi, tunda bai yarda ya girmama doka ba."
 
Tun dai bayan da kasuwancin finafinan Kannywood ya fara fuskantar tasgaro daga 2016 zuwa yanzu, tilas masu shirya finafinan Hausa su ka karkatar da akalar su zuwa sakin finafinan su a Youtube, kuma sun fi shirya finafinai masu dogon zango da aka fi sani da 'series'.
 
Source: Fimmagazine
 

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN