Ganduje ya dakatar da hadiminsa Salihu Tanko Yakasai saboda sukar Buhari


Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje ya dakatar da mashawarcinsa na musamman kan kafafen watsa labarai, Salihu Tanko Yakasai game da wasu 'maganganu masu kaushi da ya yi kan Shugaba Muhammadu Buhari a dandalin sada zumunta.'

Kwamishinan watsa labarai na Kano, Muhammad Garba da ya bada sanarwar yau Lahadi da rana ya ce dakatarwar ta fara aiki nan take. 

Ya ce duk da cewa hadimin gwamnan yana da ikon yin tsokaci kan batutuwa don ra'ayinsa, a matsayinsa na mutum mai rike da mukami, yana da wahalar a banbance ra'ayinsa da matsayin gwamnan a kan batutuwa da suka shafi al'umma.

Gwamnan ya gargadi masu rike da mukaman siyasa da ma'aikatan gwamnati su kiyayye yin maganganu da ka iya tada zaune tsaye da janyo cece-kuce. Tunda farko Yakasai ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa: "Ban taba ganin gwamnati mara tausayi ba kamar irin ta Buhari.

Lokuta da yawa mutane suna shiga mawuyacin hali kuma suna bukatar ya basu kwarin gwiwa cewa yana daukan matakai a kai amma baya yin hakan. 

Halin ko-in-kula da ya ke dashi na daban ne." A wani rubutun da ya wallafa a Twitter: "Yi wa al'ummar ka magana kan abubuwan da ke damunsu ya zama tamkar alfarma ka ke musu.

Ka gaza ware ko da minti biyar ka kwantar wa mutane hankali, mutanen da ka bi jihohi 36 ka nemi kuri'arsu, abin takaici ne wannan." A wani labarin daban, ana fargabar a ƙalla mutum 10 ne suka mutu yayinda wasu 30 suka jikkata sakamakon hadarin wasu treloli biyu suka yi a Adamawa a ranar Asabar.

Wani ganau ya shaida wa wakilin Daily Trust cewa trelolin suna tafiya ne kan titin Mayobelwa - Ganye a jihar Adamawa kuma suka yi karo sakamakon kwacewa ɗaya daga cikin direbobin da motar tayi.

Source: Legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN