Dan gidan fursuna da ya tsere ya kashe wanda ya bada shaida a kan shi a kotu


Yan sanda sun samu nasarar damkar daya daga cikin fursinoni 1,993 da suka gudu daga gidan gyaran halin Oko da Benin, sakamakon kashe wani da yayi.

The Cable ta ruwaito yadda fursinoni suka gudu sakamakon rikicin zanga-zangar EndSARS.

Yayin da suka jera wadanda ake zargin masu laifi ne guda 126 a ranar Laraba, Babatunde Kokumo, kwamishinan 'yan sandan jihar, ya ce 10 daga cikinsu fursinoni ne da suka tsere.

Ya ce 'yan sanda sun samu nasarar kara damkar fursunonin da suka koma aikata laifuka.

Dan gidan fursuna da ya tsere ya kashe wanda ya bada shaida a kan shi a kotu. Hoto daga thecable.ng

A cewarsa, "Mun zage damtse wurin neman masu laifi. Kuma ina so kusan cewa yanzu haka mun samu nasarar damkar 10 daga cikin fursunonin da suka tsere daga gidan gyara halin Oko da na Benin.

"Daya daga cikin fursunonin gidan gyara halin Oko, ya koma kauyensu a ranar don kashe wanda yayi shaidarsa a laifin da ya kai shi ga shiga gidan gyaran halin.

"Wasu 3 daga cikinsu kuma sun je yin kwacen wata mota kirar Lexus, yayin da 'yan sanda suka damkesu."

A cewarsa, "Wasu biyu sun sace wata mota kirar Toyota. Kuma dama a gidan gyaran halin suka hadu. Rundunar 'yan sanda da ke Okada, jihar Edo ne suka kama su. Yanzu haka su 10 kenan aka kama.

"An samu nasarar amsar bindigogi daga hannun 'yan ta'addan."

A wani labari na daban, a taron da FEC tayi wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta, ya amince da biyan Naira Biliyan 4.5 don samar da takardun jarabawa da kuma gyaran titinan da ke kauyakun babban birnin tarayya, Abuja.

Ministan ilimi, Malam Adamu Adamu, ya sanarwa manema labaran cikin gidan gwamnati, tare da ministan labarai da al'adu, Lai Mohammad, inda yace an ware Naira biliyan 2.9 don samar da kayan jarabawa.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/J9zhUeQqg52KIxyFnYByJN

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN