Cikakken labari: Dalilin Gwamnonin Jihohi 36 na kai Shugaba Buhari gaban Alkali


Sababbin karin bayanai sun kara fitowa game da dalilin da ya sa gwamnonin jihohi 36 su ka shigar da gwamnatin tarayya kara a gaban kotun koli.

A lokacin da shugaban kasa ya sa hannu a doka mai lamba ta 10, ya dogara ne da sashe na 5 da na 121 (3) na kudin tsarin mulkin Najeriya na shekarar 1999.

A dokar kasa, kotun koli ce ta ke da ikon raba gardama tsakanin gwamnatin tarayya da na jihohi.

Da wannan doka da gwamnatin Muhammadu Buhari ta kawo, ana sa rai kotuna za su fi samun cikakken ikon aiwatar da duk ayyukansu kai-tsaye.

Kamar yadda Ministan shari’a, Abubakar Malami SAN ya bayyana, za a rika zare kudin kotunan jihohi kai tsaye daga cikin kudin gwamnati na FAAC.

Hakan ya na nufin duk jihar da ta ki fitar wa bangaren shari’a kudinta, gwamnatin tarayya za ta dauki mataki da kanta, ta zare wannan kudi daga asusu.

Gwamnoni sun ce wannan sabuwar doka ta ci karo da wasu sassa na kundin tsarin mulki, domin gwamnatin tarayya ke dawainiya da kotunan tarayya.

Haka zalika shugaban kasa aka bar wa nauyin kotunan daukaka kara, da manyan kotunan shari’a.

Gwamnonin jihohi sun kai karar gwamnatin tarayya ne ta hannun Austin Alegeh SAN da wasu manyan Lauyoyi, daga ciki har da masu mukamin SAN.

Wata lauyar da ta tsayawa jihohi, Chinweoke Onumonu, ta bayyana cewa gwamnatin tarayya ta bar gwamnoni da wahalar kudin da kotuna su ke batarwa.

Bayan albashin da gwamnatin tarayya ta ke warewa Lauyoyi ta karkashin majalisar NJC, gwamnonin su na kukan an bar su da tarin dawainiya.

Dawainiyar da gwamnonin su ka ce su na yi sun hada da gina dakunan shari’a, gidajen Alkalai da sayen kayan aiki, tare da sayen motoci da dai sauransu.
Dokar da aka kawo ta sa duka Gwamnoni sun yi tarayya wajen adawa da gwamnatin tarayy.

Source: Legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN