Buhari ya sha alwashin ladabtar da gurbatattun jami'an SARS, ya ba matasa haƙuri


Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Litinin, 12 ga watan Oktoba, ya yi jawabi karo na farko kan soke rundunar yan sandan SARS. A wani jawabi mai tsawon kimanin mintina biyu da ya wallafa a shafinsa na Twitter, shugaban kasar ya ce soke rundunar matakin farko ne a sauye-sauye masu kamari da zai aiwatar kan aikin yan sanda.

Ya e zai yi hakan ne don tabbatar da ganin cewa jami’an tsaro sun yi aikin da ya kamata da ba rayuka da dukiyoyi kariya. Shugaban kasar ya ce za a hukunta jami’an rundunar da aka soke wadanda aka samu da aikata laifi.

Buhari ya kuma yi umurnin bincike a kan kisan wani matashi a jihar Oyo yayin zanga-zangar da aka gudanar kwanan nan. Ya kuma ce gwamnatin Najeriya ta damu da koken yan kasar kan amfani da karfi fiye da kima da yan sanda ke yi tare da kisa mara dalili. Har ila yau Shugaban kasar ya ce aikin dan sanda shi ne ya kare yan kasa saboda haka ba za a lamunci wasu yan kadan ko bata gari su kasara kimar aikin ba a Najeriya.

Ya ce: “Soke rundunar SARS mataki na farko ne a sauye-sauye masu tsauri na yin garambawul a aikin yan sanda domin tabbatar da cewar aiki muhimmin aikin yan sanda da sauran hukumomin tsaro shine kare rayuka da dukiyoyin jama’armu. “Za mu tabbatar da ganin cewa an hukunta wadanda ake zargi da hannu a cin zarafi.

“Mun yi bakin ciki da rasa ran wani matashi a jihar Oyo a yayin zanga-zangar kwanan nan. “Na yi umurnin bincike a kan abunda ya haddasa mutuwarsa. “A halin yanzu, yana da matukar muhimmanci mu gane cewa mafi yawancin jami’an rundunar yan sanda sun kasance hazikai sannan suna jajircewa kan aikinsu."

Source: Legit



Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN