An kama wani dansanda bayan ya harbi budurwarsa da bindiga a baki kuma ya tsare ranar 8 ga watan Satumba a birnin Lagos.
ISYAKU.COM ya samo cewa dansandan ya harbi dudurwarsa mai suna Joy Eze da bindiga ne lokacin da suke zazzafar cacan baki tare da ita, sai ya sa bindiga ya harbe ta a baki, daga bisani ya gudu. Bakin Joy ya yage sakamakon harbin, kuma aka garzaya zuwa Asabiti da ita.
Kakakin yansanda jihar Lagos Muyiwa Adejobi ya sanar da haka a sanarwa da ya fitar, ya ce an kama SGT Eze Aiwansone na sashen yansandan tsaron lafiya SPU Base 16 da ke Ikeja.
Adejobi ya ce SGT Eze ya gudu bayan ya aikata barnar, amma wani yayansa ne ya kamo shi ya kawo shi gaban yansanda domin shi ma Safeton yansanda ne.
https://chat.whatsapp.com/
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari