Yanzu yanzu: Zanga zanga ta sake barkewa a jihar Katsina, mutum 1 ya mutu



An rasa mutum daya daga cikin mazauna garin Jibiya da su ka shirya zanga-zanga a sanadiyyar matsalar rashin tsaro da ke addabar yankin na jihar Katsina. Jaridar Daily Trust ta fitar da rahoto a jiya cewa al’ummar Jibiya sun yi zanga-zanga domin nuna rashin jin dadin abin da ke faruwa na yawaitar kashe-kashe.


Wajen wannan zanga-zanga, an harbe wani mutumi, wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwarsa. Rahotanni sun ce an jami'ai sun kama mutane akalla 43 a jiyan Ana zargin dakarun ‘yan sandan Najeriya da aka tura su lafar da wannan zanga-zanga ne su ka harbi wannan Bawan Allah a ranar Litinin, 28 ga Satumba, 2020.


Wani ‘danuwan marigayin wanda ya bayyana sunansa da Abdulhadi, ya yi magana da ‘yan jarida yayin da ya ke kuka, ya ce ‘yan sanda sun kashe masa ‘danuwa. “Kanina ne, an kashe shi.” Inji Abdulhadi. Wani mutumi da ya fito daga kauyen Daddara, mai suna Falalu Abba, ya bayyana cewa dole ta sa talakawan yankin su ka fita zanga-zanga domin nuna bacin ransu.


"A ranar Lahadi, kwana 39 kenan a jere, kullum sai an kai hari. Idan aka kira jami’an tsaro, sai su ki zuwa mutane sun gaji don haka su ka dauki doka a hannunsu.”


Bayan Abba, wani mazaunin Jibiya, garin da ke kan iyaka da Kasar Nijar, Muhammad Bello, ya na cikin wadanda su ka fita wannan zanga-zanga da aka yi. Shi ma Abba ya ce al’umma su na fuskantar hare-hare, amma babu abin da aka iya yi wa miyagun


Source: Legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN