Yadda karamar yarinya ta sanar da mahaifinta yadda mahaifiyarta ke lalata da makwabcinsu idan baya nan


Hira ta barke tsakanin wani mahaifi da karamar diyarsa wanda ya jawo asirin matarsa ya tonu har ta kai ga sanadiyyar mutuwar aurensu na shekara 14. Bayan Steven ya dawo gida sai hira ta barke tsakaninsa da diyarsa har ya tsinci wata magana daga cikin hirarsu.


Yarinyar ta sanar da mahaifinta cewa mahaifiyarta ta shiga gidan makwabta. Mutumin ya cigaba da yiwa diyar tasa tambayoyi, har tace ma sa a lokacin da ta dawo gida ta fara neman mahaifiyar ta ta, sai makwabcinsu ya leko da kansa yace mata yanzu mahaifiyarta zata iso gareta. 

 

Hakan ya jawo rikici tsakanin ma'auratan kwana daya bayan samun labarin, inda Steven ke tambayar matarsa dalilin shiga makwabta kamar yadda Jaridar Kidsport ta ruwaito.


Da farko ta amsawa mijin nata sama-sama, sai dai sakamakon dadewar mata da mijin tare, mijin yace ya san yadda takeyi idan tayi karya. Daga baya ta fito fili tana neman afuwar mijin nata ta sanar masa da cewa a gaskiya sun taba jikin juna kuma sun sumbaci juna wa nda tasan hakan da sukayi bai dace ba.


Steven yace: "Nasan yadda take yiwa mutane karya. Kuma na tabbatar ba sumbata kadai su ka tsaya ba." Ya ce ya fatattaketa daga gidansa amma bayan yaji nasihar mutane sai ya amince ya dawo da ita saboda yaransu. Steven yace gaskiya wannan al'amari ya shafi tarayyarmu matuka. 

 

Ya kara da cewa: "Gaskiya na rikice gaba daya saboda ina kaunarta sai dai kaunar ta zama tamkar abota amma ba wai soyayyar miji da mata ba." Mutumin ya nema shawarar mutane akan al'amarin.


Daya daga cikin masu bashi shawara yace: "Ina tunanin a wannan gabar ya kamata kayi nazari mai kyau, duk da taci amanarka ka ga idan zaka iya yafe mata." Wani kuma yace "Ka nemo abinda zai sa ka manta da wannan lamarin yadda bazai shafi zuri'arku ba, duk da nasan zai dauki lokaci." 

 

Kamar yadda rahoto ya nuna, ma'aikata daga garin Fatima Dos dake Cavite suna gabatar da taro ta manhajar zoom kamar yadda suka saba a ranar Laraba.


Shugabansu Jesus Estil, wanda aka bayyana cewa bashi da ilimi akan harkokin na'ura mai kwakwalwa yaje ya danna wani wuri sai kyamarar na'urarshi ta fara aiki.

Source: Legit 



Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN