Takanas mai shekara 20 ya je Jigawa daga Sokoto domin a yi Luwadi da shi a kan N50,000

Hukumar Hisbah a jihar Jigawa ta kama wasu mutum biyu bisa zargin aikata Luwadi a Dutse, babban birnin jihar.

Wadanda aka kama sune, Adamu mai shekara 32 da Tijjani mai shekar 20. An kama su ne a wani Otel, bayan matsanancin gardama da ya kaure tsakaninsu ya tayar da hankalin makwabta , wanda suka rada wa Hukumar Hisbah. Sakamakon haka Hisbah ta tura jami'anta kuma suka kama wadannan mutane.

Kwamandan Hisbah na jihar Jigawa, Malam Ibarahim Dahiru, ya ce, " Yau 2 ga watan Satumba, jami;an mu sun yi nassarar cafke wasu mutane biyu bisa zargin aikata Luwadi a Dutse.




Wannan ya hada da wani mutum mai suna Adamu mai shekar 32 wanda ke zaune a rukunin gidaje na Unguwa Uku, a jihar Kano, ya gayyaci abokinsa mai suna Tijjani mai shekara 20, wanda ke zaune a rukunin gidaje na Garkuwa a jihar Sokoto.

Sun tsara yadda za su hadu ne a shafin Facebook, bisa alkawari da Adamu ya yi wa Tijjani cewa zai bashi N50,000 idan ya zo suka aikata Luwadi. Sakamakon haka Tijjani ya shigo mota ya zo Dutse ya sami Adamu a Otel da ya kama, kuma suka kwana tare.




Amma washe gari sai Adamu ya kasa biyan Tijjani N50,000 da ya alkawarta masa, sakamakon haka rikici ya kaure har makwabta suka farga da halin da mutanen ke ciki kuma suka sanar da hukumar Hisbah, daga bisani Hisbah ta tura jami'anta suka kama su"

Rahotu da muka samu ya nuna cewa wadanda aka kama sun amsa laifinsu , kuma za a mika su ga yansanda domin fuskantar tuhuma a Kotu.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt


أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN