Sunaye: Sojoji su cafke masu tada ƙayan baya 5 a maɓuyar tsohon shugaban ƴan bindiga

Dakarun sojojin Najeriya a ranar Litinin sun lalata maɓuyar shugaban masu tayar da ƙayan baya na Benue da aka kashe Terwase Akwaza da aka fi sani da Gana. Sun kai sumammen ne a garin Adu da ke Chanchanji a ƙaramar hukumar Takum da ke jihar Taraba. Sun kuma kashe masu tayar da ƙayan baya biyu sun kuma wasu biyar da ake zargin ƴan bindiga ne.



Wadanda aka kama sun hada da Saalu Terlumun, Benjamin Valentine da Milton Gbegi da aka kama a jihar Benue. Sai kuma Isaac Hilega da aka yi wa lakabi da Bawasa da Godwin Terwase da aka kama a Chanchanji a jihar Taraba. Sojojin sector 2 da aka girke a Gbise a ƙaramar hukumar Katsina-Ala na jihar Benue da sojojin sector 4 ne suka yi haɗin gwiwa suka kai sumamen da Adu. A yayin sumamen, sojojin sun yi arangama da masu tada ƙayan baya da suka buɗe musu wuta a yayin da suka kusa isa maɓuyar.



A cewar sanarwar da kakakin Hedkwatan Tsaro, John Enenche ya fitar, sojojin sun mayar wa ƴan tada ƙayar bayan wuta suka ci galaba a kansu hakan yasa suka tarwatsa da raunukan bindiga. Kazalika, Sojojin sun kuma yi nasarar kwato bindigu ƙirar Pistol. Sanarwar har ila yau ta ce Sojojin na Operation Whirl Stroke sun kwato wayoyin salula 16 da layu da wani ganye da ake zargi wiwi ne.



"Wadanda ake zargin suna amsa tambayoyi daga bisani za a mika su ga ƴan sanda domin cigaba da bincike. A halin yanzu sojoji sun mamaye unguwar suna sintiri domin hana miyagun saƙat," a cewar hedkwatar tsaro, DHQ.

Source: Legit

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN