Sultan ya yi magana kan kashe-kashen kudancin Kaduna, duba abin da yace

Sa’ad Abubakar III, Sultan na Sokoto, ya yi kira ga kawo karshen kashe-kashe a kudancin Kaduna. Yankin ta fuskanci yawan hare-hare da ya yi sanadiyar rasa rayuka da dukiyoyi. Da yake magana a taron kungiyar sarakunan arewa a Kaduna a ranar Litinin, 7 ga watan Satumba, basaraken ya bayyana rikicin a matsayin “hauka da ya zama dole a dakatar dashi cikin gaggawa”.


Ya yi kira ga wadanda ke da hannu a kashe-kashen da su daina mummunan aika-aikan, inda ya ce “hakan ya ishe su.” Sultan ya ce: “babu wani mutum da ke cikin hankalinsa da zai je yana kashe-kashen bayin Allah bisa ko wani hujja. Basaraken ya kuma zargi yan siyasa da rura wutar rikicin, inda ya roki yan Najeriya da kada su bari a mayar da su karen farauta, jaridar The Cable ta ruwaito.


“Idan kuka ci gaba da rura wutar kashe-kashen saboda banbanci kabila ko addini toh bayin Allah ake kashewa yayinda ake kare masu mulki” in ji shi. Nasir El-Rufai, gwamnan jihar Kaduna, ya ce rikicin kudancin Kaduna ya samo asali tun rikicin Kasuwan Magani na farko da aka yi a karamar hukumar Kajuru a 1980. Ya ce gwamnatinsa na ta kokarin ganin ta kawo karshen kashe-kashen da dawo da zaman lafiya.


Gwamnan ya kara da cewa an samar da wani sansanin sojoji da tashar yan sandan tafi da gidanka a yankin yayinda aka tura rundunar tsaron sama yankin. Ya ce ana amfani da kayayyaki kamar su jirage marasa matuka da na’urar gano lambar waya wajen kashe yan bindiga a jihar.


A wani labarin, rundunar Operation Accord sun kashe wasu ‘yan bindiga hudu a yankin Jeka Da Rabi da ke hanyar babbar titin Kaduna-Abuja a jihar Kaduna sannan sun samo makamai daga hannunsu. Shugaban sashin labarai na rundunar tsaro, Manjo Janar John Enenche ne ya tabbatar da hakan a cikin wani jawabi da ya fitar a ranar Alhamis.

Source: Legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt



أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN