Alkali Salami ya kori lauyoyin Magu yayin zaman kwamitin bincike


An fara samun matsala ne bayan Wahab Shitu, shugaban tawagar lauyoyin Magu, ya mike domin gabatar da sauran abokan aikinsa. Sai dai, Salami ya katsewa Shittu hanzari ta hanyar sanar da shi cewa shine kadai za a bari ya kare Magu.


Bayan hakan ne sai ya umarci jami'an tsaro su fitar da sauran lauyoyin. A ranar Laraba, 15 ga watan Yuli, aka saki Magu bayan ya shafe sati biyu a tsare a hedikwatar rundunar 'yan sanda.


Magu ya fara gurfana a gaban kwamiti bincike a ranar Litinin, 6 ga watan Yuli, kuma tun daga ranar wasu jami'an 'yan sanda su ka yi awon gaba da shi zuwa hedikwatarsu. An fara binciken Magu ne bisa zarginsa da almundahana da kuma rashin biyayya, kamar yadda ministan shari'a, Abubakar Malami, ya rubuta korafi a kansa zuwa fadar shugaban kasa.


Har yanzu kwamitin Salami ya na cigaba da gudanar da bincike a kan Magu duk da an bayar da shi beli. Shugaba Buhari ya kafa kwamitin ne domin gudanar da bincike tare da kwato kadarorin gwamnati daga hannun wasu manyan jami'an gwamnati; na baya da na yanzu, da ake zargi da almundahana, waskiya, ko sama da fadin kudi, dukiya ko wata kadara mallakar gwamnati.

Source: Legit



Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN