Mutum mafi muni a fadin duniya ya aura mata ta 3 (Hotuna)

Bahaushe yana cewa so gamon jini, tabbas hakan ya tabbata a kan wani mutum wanda ake cewa yafi kowa muni a duniya. Godfrey Baguma mai wasan bada dariya ne a kasar Uganda, kuma an fi saninsa da Ssebabi. Mafi munin mutumin a fadin duniyar ya aura masoyiyarsa a matsayin mata ta uku a wani irin kasaitaccen biki mai cike da shagali.

An daura auren masoyan inda suka zama mata da miji. Babu shakka suna cike da farin ciki inda suka dinga daukar hotunan da suka karade kafafen sada zumuntar zamani. Godfrey Baguma, mai shekaru 47, yana fama da wani irin ciwo ne wanda har yanzu ba a gano kansa ba.


A shekarun da suka gabata, matarsa ta biyu mai suna Kate Namanda mai shekaru 30 ta haifa yarinya mace. Baguma ya samu nasarar lashe wata gasa a 2002, bayan ya shigeta domin samarwa iyalansa kudi, jaridar The Nation ta wallafa.


Kafin aurensa da Kate, Godfrey yana da mata daya da yara biyu, amma auren ya rabu bayan da ta kama shi yana cin amanarta. Ssebabi yana da 'ya'ya bakwai. Ya samu sunansa Ssebabi bayan nasarar da yayi wurin lashe gasar zama mutum mafi muni a duniya. Yana rayuwa a Kyawanga da ke yankin Lwengo, kuma yana da 'ya'ya biyar da Kate Namande.

Source: Legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN