Mutum 20 sun mutu a harin da ISWAP ta kai wa tawagar gwamnan Borno

 


'Yan bindiga da ake zargin 'yan kungiyar ISWAP ne a ranar Juma'a sun kai wa tawagar ma'aikatan gwamnatin jihar Borno hari inda suka kashe mutum 30 ciki har da jami'an tsaro 17 a hanyarsu ta zuwa Bama a Borno a cewar majiyoyi.


Mutane da dama kuma sun samu rauni sakamakon harin da 'yan ta'addan suka kai wa tawagar. Wani majiya daga hukumomin tsaro ta ce abinda ya faru sakamakon harin lamari ne mai tayar da hankali. "An tabbatar da mutuwar 'yan sanda 12, sojoji 5, farar hula 13, mambobin JTF hudu.


Yan ta'addan sun kuma kwace motar 'yan sanda mai bindiga daya, motan sojoji mai bindiga daya da motoccin daukan kaya shida mallakar gwamnatin jihar Borno," a cewar majiyar tsaron.


"An dakile harin nan take amma muna zargin ISWAP ce ta kai wa tawagar gwamnatin jihar hari a hanyarta na zuwa Baga don aikin mayar da 'yan gudun hijira," a cewar majiyar tsaron.


Wata majiyar daban ta ce harin ya faru ne wasu kilomita kadan daga hedkwatan MJTF da ke Baga, inda ya kara da cewa an kai wadanda suka yi rauni babban asibitin Monguno. A watan Yulin wannan shekarar, an taba kai wa Gwamna Zulum hari tare da tawagarsa a kusa da wannan wurin a hanyarsa na dawowa daga Baga.


Gwamnan Borno, Babagana Zulum ya lashe kyautar Zik a rukunin shugabanci na shekarar 2019 kamar yadda Farfesa Pat Utomi ya sanar a ranar Alhamis. Zulum wanda shine mutum na takwas cikin jerin wadanda suka lashe kyautar an karrama shi ne saboda shugabanci na gari.


Source: Legit




Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN