Mata 10 sun mutu sakamakon hatsarin Kwale-kwale a karamar hukumar Jega jihar Kebbi

Mutane goma sun mutu a wani kifewar kwale-kwale da ya afku a ranar Litinin, a karamar hukumar Jega da ke jihar Kebbi, jaridar Daily Trust ta ruwaito. Bincike ya nuna cewa mamatan wadanda suka kasance mata na a hanyarsu ta zuwa bikin aure ne daga Madauci zuwa kauyen Tungan Gehuru. Kwale-kwalen ya kife ne da misalin karfe 4:00 na rana a ranar Litinin yayinda yake dauke da fasinjoji 10.

Da yake hira da jaridar Daily Trust ta wayar tarho, shugaban karamar hukumar, Barista Shehu Marshal; ya tabbatar da faruwar lamarin cewa tuni aka samo gawarwakin mutum hudu. “An samo gawarwakin mutum hudu kuma tuni aka binne su.

Tawagar ceto na aiki domin nemo sauran mutane shida” in ji Marshal. A wani labari makamancin haka, mun ji a baya cewa wasu mutum uku da aka bayyana a matsayin Melody M, Isaac G., da James S., sun mutu a wani hatsarin jirgin ruwa da ya afku a jihar Adamawa.

Shafin Linda Ikeji ya ruwaito cewa mutanen, wadanda suka kasance maza biyu da mace guda, sun nitse ne a yayinda suke a hanyarsu ta zuwa bikin binne wani a karamar hukumar Lamurde bayan kwale-kwalen ya kife. Da yake tabbatar da lamarin, Shugaban karamar hukumar Lamurde, Burto Williams, ya bayyana lamarin a matsayin abun bakin ciki.

“Hatsarin abun bakin ciki ne da yake bukatar gwamnati ta kawo agaji ga mutanen yankin wadanda ruwa ke yawan yi wa barna. “Karamar hukumar Lamurde na kokarin samar da kulawar likitoci ga wadanda suka tsira yayinda hukumar za ta dauki nauyin birne mutum uku da suka mutu,” in ji Burto.

Source: Legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN