• Labaran yau


  Kungiyar IPOB ta kai hari unguwar Hausawa, ta kashe Hausawa biyu a jihar Ribas

  Hausawa mazauna Jihar Ribas sun rasa mutum biyu a garin Oyigbo, bayan da aka zargi kungiyar masu fafutukar kirkirar Biyafara (IPOB) da kai musu hari.


  Rikicin wanda ya faru a ranar Lahadi ya kuma jikata wasu mutum biyu.


  Wani ganau, ya bayyana wa Aminiya cewar, a ranar Asabar zuwa Lahadi ne wasu da ake zargin ‘yan kungiyar IPOB ne dauke da miyagun makamai suka kai hari a unguwar Hausawa.

  Ya ce sakamakon harin da aka kai, “Mutum biyu sun rasa rayukansu, yayin da aka ji wa wasu biyu munanan raunuka”.


  Mai magana da yawun Hausawa mazauna Jihar Ribas, Alhaji Musa Saidu, ya tabbatar was wakilinmu aukuwar lamarin.


  Saidu ya ce wasu matasa da ake zargin ‘yan kungiyar IPOB ne dauke da makamai suka kai hari a wani wuri da mafi yawanci mutanen Hausawa ne, a Oyigbo, sakamakon haka aka kashe samarin biyu.


  Ya ce sakamakon harin wasu kananan ‘yan tireda biyu sun samu munanan raunuka.

  Source: Aminiya


  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari


  Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt


  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Kungiyar IPOB ta kai hari unguwar Hausawa, ta kashe Hausawa biyu a jihar Ribas Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama