Gaba daya fasinja sun mutu bayan motar bas ta yi hatsari ta kama da wuta

Mutane da ba tantance adadinsu ba sun mutu bayan sun kone kurmus ta yadda ba za a iya gane mutum ba , bayan motar bas mai daukan mutum 18 da suke ciki ya yi hatsari ya yi ta mulmula a kasa kuma ya kama da wuta a kan hanyar Onitsha zuwa Owerri a jihar Anambra da ke kudu maso gabashin Najeriya ranar Lahadi.


Mutum kwaya daya tilau da motar ta jefo waje lokacin da take mulmula a kasa shi ma ya mutu, kuma an kai gawarsa wani Asibiti da ke kusa, inda aka aje gawarsa a dakin aje gawaki a cewar hukumar kiyaye hadurra ta kasa FRSC.


Kwamandan hukumar FRSC na jihar Anambra, Andrew Kumapayi ya ce hatsarin ya faru ne tsakanin Amoka, a kan tagwayen hanyar Onitsha zuwa Owerri.



Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt


أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN