Ko dadadden ciwo na iya sa dan adam yanke shawara cewa ya kashe kansa?


Hukumar Lafiya ta Duniya, wato WHO a taƙaice, ta ce duk daƙiƙa 40 mutum guda na kashe kansa. Saboda haka, aƙalla mutane 800,000 ne ke kashe kansu duk shekara kuma alƙaluman da ƙara ƙaruwa a sassan duniya.

Ƙungiyar Kiyaye Kashe Kai ta Ƙasa-da-ƙasa ce ta ware duk ranar 10 ga watan Satumban kowacce shekara don gangamin wayar da kai kan kashe kai, da ma samo hanyoyin magance ƙaruwar kashe kai a faɗin duniya wanda gangamin ke gudana ƙarƙashin kulawar Hukumar Lafiya ta Duniya.

Bincike da dama sun nuna yadda fama da daɗaɗɗen ciwo (matsanancin ciwo tsawon wata uku ko fiye) ke cikin jerin matsalolin da ke ingiza mutane kashe kansu don su huta da ciwo. Larurorin da ke haifar da fama da daɗaɗɗen ciwo sun hada da ciwon sikila, ciwon daji/kansa, ciwon laka, ciwukan gaɓoɓi kamar ciwon baya, ciwon gwiwa da suransu.

A yayin da ake bikin wannan rana a yau, likitocin fisiyo a faɗin duniya na ci gaba da duƙufa wajen samo nagartattun hanyoyin magance dadaɗɗen ciwo daga waɗancan ciwuka ba tare da shan magani/ƙwaya ko yin allura ba.

Idan ba a manta ba, a ranar 31 ga watan Agustan da ya wuce ne aka gudanar da ranar wayar da kai kan aringizon magani ta duniya, inda Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce "shan ƙwayoyi dangin hodar ibilis na ƙara ƙamari a ƙasashe da dama wanda ƙaruwar amfani da ƙwayoyin ke da nasaba da fama da daɗaɗɗen ciwo".

Source: Physio Hausa


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN