Farin jinin da Buhari ke da shi wurin talakawa ya bani mamaki - Rarara


Dauda Kahutu Rarara ya shahara sosai saboda yi wa Shugaba Muhammadu Buhari wakoki na yabo. A makon da ta gabata, ya wallafa sako a dandalin sada zumunta inda ya bukaci magoya bayan shugaba Muhammadu Buhari su tallafa masa da Naira dubu dai-dai domin ya fitar da sabuwar album dinsa. Na sha mamaki, ban taba sanin haka Buhari ke da farin jini ba a cewar mawakin bayan ganin irin adadin kudin da aka tara masa.


Rarara ya ce ya gaji da jin maganganun da mutane ke yi a kan wakar da zai fitar inda zai lissafo ayyuka fiye da 192 da gwamnatin Buhari ta aiwatar a sassan kasar nan. Da ya ke hira da Daily Trust a Kano, Rarara ya ce ya yanke hukuncin fitar da wakokin ne saboda ikirarin da wasu ke yi na cewa 'yan Najeriya sun juya wa Shugaba Muhammadu Buhari baya.


Rarara bai ambaci adadin kudin da ya samu ba a halin yanzu amma ya ce raini ne hasashen da wasu ke yi na cewa Naira miliyan 70 aka tara masa kawo yanzu. "Cewa Naira miliyan 70 aka tara domin mutum mai muhimmanci kamar Shugaba Muhammadu Buhari ma ai cin fuska ne, mutane ma suna son bayar da fiye da N1000 amma mu na fada musu dubu dayan kawai muke bukata. Bayan sun bayar da dubu dayan za su kuma nemi suyi kari. Ban taba ganin wani shugaba da mutane ke kauna kamar shi ba," in ji shi.


Ya kara da cewa bai riga ya sanar da duniya adadin kudin da al'umma suka tara ba domin yi wa Shugaba Buhari sabbin wakokin yabon. "Nan gaba za mu fada wa duniya abinda muka tara domin yi wa Shugaba Buhari wakar. Za mu kira taron manema labarai mu shaida wa duniya abinda muka samu kuma mu shaidawa 'yan adawa da ke yada karya cewa an dena yayin Buhari cewa har yanzu talakawa na kaunar sa," in ji shi.


Wasu 'yan Najeriya sun soki matakin da Rarara ya dauka na cewa mutane su tara masa kudi ya yi wa Buhari waka domin nuna wa duniya cewa har yanzu suna kaunar shi. Shugaban jam'iyyar APC na jihar Adamawa, Alh. Ibrahim Bilal, ne ya tabbatar da hakan a ranar Asabar a garin Yola kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Source: Legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN