Duba illar da ambaliyar ruwa a jihar Kebbi zata yi wa Najeriya

A ranar Laraba ne shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya fitar da sakon jaje ga jama'ar jihar Kebbi a kan asarar rayuka da amfanin gona da ambaliyar ruwa ta haifar a jihar.

Da ya ke mika sakon ta'aziyya ga wadanda su ka rasa wasu nasu sakamakon ambaliyar, Buhari ya bayyana cewa asarar kayan amfanin gona za ta shafi wadatuwar kayan abincin da ake nomawa a gida Najeriya. Buhari ya bayyana hakan ne a cikin jawabin da ya fitar ta hannun babban kakakinsa, Malam Garba Shehu.

"Shugaba Buhari ya jajantawa jama'ar jihar Kebbi da ambaliyar ruwa ta halaka 'yan uwansu tare da lalata musu gonakinsu. "Wannan ambaliya ba kankanin koma baya za ta haifarwa Najeriya ba ta fuskar abincin da ake nomawa a cikin kasa, za ta kawo nakasu ga kokarin gwamnati na ganin an samu wadatuwar kayan abinci, musamman shinkafa.

"Jihar Kebbi ta na daga cikin jihohin da wannan gwamnati ta dogara da su domin cimma manufarta na noma shinkafar da za ta wadata Najeriya," a cewar wani bangare na jawabin shugaba Buhari.

Ambaliyar ruwan sama ta yi sanadiyar mutuwar mutane 6 tare da lalata gonakin dumbin manoma a jihar Kebbi. An yi kiyasin cewa ambaliyar ruwan ta lalata amfanin gona na biliyoyin Naira. Shugaba Buhari ya bayar da tabbacin cewa gwamnatin tarayya za ta hada kai da gwamnatin Kebbi domin ganin cewa an tallafawa manoman da ambaliyar ruwan ta yi wa barnar amfanin da suka shuka gonakinsu.

Source: Legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN