Da duminsa: Oshiomole ya lallasa PDP a akwatinsa da tazara sama da 1200


Tsohon shugaban jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Adams Aliyu Oshiomole, ya yi nasara a rumfarsa na tazara fiye da na ko ina kawo yanzu a jihar. Jam'iyyar APC ta samu kuri'u 1,201 a gunduma ta 10, akwati mai lamba 001 na karamar hukumar Estako West a yau Asabar. Jam'iyyar PDP ba ta samu kuri'a ko kwaya daya a akwatin gidan Oshiomole ba, bisa sakamakon da aka sanar.

Sakamakon gidan Oshiomole ta baiwa APC dama toshe gurbin da PDP ta zarce mata a karamar hukumar duk da cewa mataimakin gwamnan jihar, Philip Shaibu dan gari daya ne da shi. Tun da akwai gunduma 12 a karamar hukumar Estako West, har yanzu ba za'a iya fadin wanda zai yi nasara tun akwai saura kuri'un da ba'a kirga ba. PREMIUM TIMES ta ruwaito yadda aka biya mutane kudi su kada kuri'a a rumfar zaben Oshiomole, kamar yadda akayi a wasu wurare da dama.


Yan jaridar da suka yi kokarin daukan hoton hakan sun fuskanci wulakanci daga hannun matasan dake wajen. Ize-Iyamu ta lashe akwatin inda ya samu kuri'u 292 kuma Godwin Obaseki ya samu kuri'u 0. Hakazalika Dan takaran jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP, Godwin Obaseki, ya lashe rumfar zabensa dake akwati ta 17, makarantar firamaren Emokpae, karamar hukumar Oredo. Yayinda Obaseki ya lashe akwatinsa da kuri'u 184, Ize-Iyamu ya samu kuri'u 62.

Source: Legit



Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN