Yadda wata amarya ta haifi Jarirai uku lokaci daya a Birnin kebbi jihar Kebbi

Wata mata ta haifi yara Jarirai yan uku a Asibitin haihuwa na Fati Lami da ke garin Birnin kebbi babban birnin jihar Kebbi ranar Alhamis.

Mahaifin Jariran Malam Sirajo Umaru, ya bayyana irin farin ciki da ya shiga bayan sako ya same cewa mai dakinsa wacce suka shafe shekara hudu suna zaman aure ta haifa masa yara Jarirai maza guda uku.

Jarirai da aka haifa
Malam Umaru wanda ke zaune a unguwar Filin Sarki a tsohon garin Birnin kebbi, ya ce " Ranar Alhamis da misalin karfe 10:30 aka sanar da ni cewa iyalina sun haihu, an sanar da ni cewa ta haifi yara uku kuma duka maza. Sai na Gode wa Alah da ya nuna mani wannan ranar. Kuma an haife su lafiya kalau kuma uwarsu ta nan lafiya su ma Jariran lafiya kalau".

Ya ce " Wannan ne karo na farako da aka haifa mani Jarirai, tun da nake, ba a taba haifa mani tagwaye ba tun lokacin da na yi aure har zuwa yanzu. Amma cikin ikon Allah ga shi yanzu Allah ya bani yara uku lokaci daya, kuma duka maza".

Malam Sirajo Umaru mahaifin Jarirai 3 da aka haifa
Malam Umar ya kuma ce yanzu shekara hudu kenan na zaman aurensu da mai dakinsa, kuma sun haifi yarinya daya tare da amaryarsa kafin wannan lokaci.

Ya ce " Ina godiya ga Ubangiji, na gode wa Allah da ya nuna mani wannan rana, kuma an haife su lafiya kalau, ina yi wa kowa fatan alhairi. Ina kuma fatar duk mace da ke nakuda a wannan Asibiti ta haihu lafiya kalau. kuma ina kara nuna farin ciki na da wanna kyauta da Allah ya bani, ina cikin jin dadin rayuwa da farin ciki".

DAGA ISYAKU.COM

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN