Wayoyin Tecno da China ke sayarwa a Afirka na satar bayanan masu su

An gano wata manhaja cikin dubun dubatan wayoyin hannu da ake sayarwa a nahiyar Afirka da kan yi wa masu waya rajista a shafukan intanet ba tare da amincewarsu ba.
Wani kamfanin samar da tsaro mai binciken fasahar sadarwar zamani mai suna Upstream ya gano manhajar da aka saka cikin wayoyi 53,000 samfurin Tecno da ake sayarwa a kasuwanni da ke kasashen Afirka kamar Habasha da Kamaru da Masar da Ghana da kuma Afirka ta Kudu.
Amma Transsion, wanda shi ne kamfanin da ke kera wayoyin na Tecno ya ce an saka manhajar ce ba tare da saninsa ba.
Sai dai kamfanin Upstream ya ce manhajar na cutar da yawancin "mutanen da ba su da karfin tattalin arziki" sosai.
"Ganin cewa manhajar na shiga hannayen mutanen da marasa galihu ne wadanda suka sayi miliyoyin wayoyin tare da manhajar zai tabbatar da halin da kasuwar wayoyin ke ciki a halin yanzu," inji Geoffrey Cleaves, shugaban Secure-D, bangaren bincike na kamfanin Upstream.
Manhajar na boyewa cikin wayoyin hannu samfurin Android inda daga nan ta kan rika shigar da wani umarni mai hatsari da kan aika da sakonni ga wasu kamfanoni na dabam cewa mai wayar na bukatar ayi masa rajista, kuma duk wannan na faruwa ne ba tare da sani ko amincewar masu wayar ba.
Bayan an yi nasarar yi wa wayar rajista, daga nan za ta riƙa kwashe datar da mai wayar ke loda wa, wadda ita ce hanyar da yawancin mutane a nahiyar Afirka kan sayi data.
A takaice, kamfanin Upstream ya gano abin da ya kira irin wannan "mugunyar halayyar" cikin wayoyin Tecno fiye da 200,000.
Wani bincike na daban da kamfanin IDC ya gudanar ya gano cewa Transsion Holdings ne kamfanin da ke kan gaba wajen kera wayoyin hannu a China kuma shi ne yafi cinikin wayoyin hannun a fadin nahiyar Afirka.
A martanin da suka mayar kan tuhumar da BBC ta yi mu su na cutar da masu amfani da wayoyin hannu, kamfanin Tecno Mobile ya ce "ai wannan tsohuwar matsala ce da tuni aka sha karfinta a kasashen duniya" kuma a watan Maris na 2018 ma tayi maganin matsalar a wayoyinta.
Kamfanin Tecno Mobile ya kuma ce "mun dauki bayannan sirri na masu sayen wayoyinmu da muhimmanci," kuma "muna tantance dukkan abubuwan da ke shafar wayoyin da muke kerawa kafin su kai ga masu amfani da su."

Matsalar ta zama ruwan dare

A farkon wannan shekarar, kamfanin Malwarebytes ya sanar da cewa ya gano irin wannan manhajar mai satar bayanai da asarar data cikin wata wayar hannu ta daban - MX U686CL. An dai rika tallata wannan wayar ga iyalai marasa galihu a Amurka.
Sannan a 2016, Ryan Johnson, wani mai bincike ya gano cewa wayoyi samfurin Android fiye da miliyon 700 na dauke da manhajar da ke satar bayanai ko cutar da mai wayar ba tare da amincewarsu ba.
Kamfanin Google wanda shi ne ke samar da manhajar ta Android ya ce ya san da matsalar.
A wani bayani da ya wallafa a bara, Google ya dora alhakin bayyanar wadannan manhajojin cikin wayoyin hannu samfurin Android kan kamfanonin da ke tallata wayoyin, inda ya ce ya kama su suna saƙa manhajoji irin wadanda ke bude waya ta hanyar kallon fuskar mai ita da kuma manhajar da ke satar bayanai ta Triada.
Ya kuma ce ya yi aiki tare da masu ƙera wayoyin domin cire irin wadannan manhajojin daga wayoyin hannun da suka riga suka shiga kasuwa.
Source: BBC

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt


Previous Post Next Post

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/H5IqezEzbfJ3YScTo1dk59

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN