• Labaran yau


  Wata Mata Da Ya’yan ta sun kashe kansu bayan Mijinta ya mutu sakamakon Coronavirus

  Parimi Snuneetha mai shekaru 50 da haihuwa, rahotanni sun bayyana cewa ta kashe kanta ne tare da ‘ya’yan ta su 2 Narasaiah Phanikumar, mai shekaru 25 da kuma Lakshmi Aparna mai shekaru 23, bayan mijin ta ya mutu sakamakon cutar coronavirus, kamar yadda The Herald ta rawaito.

  Bayan mutuwar mijin nata mai suna Narasaiah mai kimanin shekaru 52 sakamakon cutar Korona, kwanaki 4 da suka gabata matar da iyalan nata suka fada cikin matsanan ciyar damuwa a sabili da ‘yan uwa da abokanai sun ki zuwa dan jajan ta musu mutuwar mijin nata tare da kaurace musu da gaba daya.

  Hakan ne ya sanya matar da yaran nata  fadowa daga kan wata gada dake a Andhra Pradesh’s Rajahmundry a ranar 19 ga watan Ogusta.

  A cewar rundunar ‘yan sanda ta bayyana cewa ta gano wata takarda da mamatan suka bari a cikin wata motar su a kusa da gadar. Inda rundunar ta bayyana cewa sun mutu ne sakamakon nuna kyama da a ke musu.

  hutudole


  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari


  Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Wata Mata Da Ya’yan ta sun kashe kansu bayan Mijinta ya mutu sakamakon Coronavirus Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama