An tabbatar da mutuwar tsohuwar ne bayan tiyata da aka yi mata domin daidaita matsalar cushewar hanji da karfe 1:10 na dare. Daga bisani aka kai gawarta dakin ajiye gawa.
Amma bayan awa bakwai, da karfe 8am na safe, sai tsohuwar ta farfado daga mutuwa, lamari da ya tsoratar da ma'aikacin dakin gawa da aka ajiye tsohuwar.
Daga bisani an lullube tsohuwarb da bargo kuma aka kai ta dakin kulawa na gaggawa a Asibitin, lamari da ya sa nan take Likitoci suka taru a kanta.
Sai dai bayanai sun nuna cewa an dakatar da likitan da ya tabbatar da mutuwarta daga aiki har sai an kammala bincike kan lamarin.
DAGA ISYAKU.COM
https://chat.whatsapp.com/
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/