• Labaran yau


  Ta bayyan cewa wasu Kanal 2 da Brigediya ne suka kitsa juyin mulki a kasar Mali

  Ta bayyana cewa wasu soji masu mukamin Kanal ne suka kitsa juyin mulki da aka yi a kasar Mali ranar Talata wanda ya kawo karshen mulkin shugaba Boubacar Keita. Sojin da suka jagoranci juyin mulkin sune Sadio Camara da Malick Diaw.Boubacar Ke.

  Haka zalika  wasu sojin da ke da hannu a juyin mulkin sun hada da Laftana kanal Mama Seku Lelenta.

  Babu takamammen bayani kan ko soji nawa ne suke da hannu gaba daya a wannan juyin mulki. sai dai ta tabbata cewa an ambato sunan Brigediya janar Cheick Fanta Mady Dembélé

  Sojin sun yi kame kamen manyan jami'an gwamnatin shugaba  Boubacar Keita da shugaban sojin tsaron kasa na National Guard Abdoulaye Daffé, Ministan kudi Tiebilé Dramé, da kuma Ministan harkokin waje . Haka zalika Dan majalisar tarayya Moussa Timbine,yana hannunsu tare da sauran manyan jami'an tsohon gwamnatin.


  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari


  Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Ta bayyan cewa wasu Kanal 2 da Brigediya ne suka kitsa juyin mulki a kasar Mali Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama