Sokoto: An ceto wani mutum da kawunsa ya rufe shi tsawon shekaru 15 ba fita

Ƴan sanda jihar Sokoto sun ceto wani mutum mai shekaru 45, Salisu Muhammad da kawunsa ya ɗaure shi a gida na tsawon shekaru 15 a Gidan Madi a ƙaramar hukumar Tangaza.

An ce Muhammad wadda ke da yarinya da ta girma yana fama da taɓin hankali ne kamar yadda Daily Trust ta ruwaito. Hajiya Ubaida Bello, mai bawa Gwamna Aminu Tambuwal shawara a kan Hakokin Bil Adama da Kungiyoyin tallafawa al'umma ce makwabta ne suka sanar da hukuma game da halin da ya ke ciki don da farko sunyi tsammanin ya mutu ne.

"Da farko sunyi tsammanin ya mutu ne domin ba su gan shi ba a waje na tsawon shekaru fiye da goma. "Da suka gano halin da ya ke ciki, sun sanar da mu cikin gaggawa.

"Daga nan ne muka tattara ƴan sanda, masu kare hakkin bil adama da wasu ma'aikatan ƙaramar hukuma ciki har da shugaban ƙaramar hukuma muka tafi gidan muka ceto shi," in ji ta

An gano wasu mata biyu a gidan ciki har da Æ´arsa mai shekaru 19 wadda a yanzu ba ta san tsawon lokacin da ya yi a daure ba. "Mun tarar da shi a cikin mummunan yanayi, yana bayan gida da fitsari a wuri guda ba tare da wani kulawa ba.

"Ya kasa yin tafiya da kansa ma saboda rashin samun abinci. "Idan suna iƙirarin cewa yana fama da taɓin hankali ne me yasa ba su kai shi asibitin ƙwaƙwalwa ba domin ayi masa magani," in ji ta.

Wata majiya ta shaidawa Daily Trust cewa kawun mutumin ne da ke zaune a wani ƙauye nan kusa ya rufe shi. Bello ta ce an garzaya da mutum asibitin ƙwaƙwalwa a karamar hukumar Ƙware yayin da ƴan sanda na cigaba da bincike don gano dalilin rufe shi.

Kakakin ƴan sandan jihar Sokoto ASP Muhammad Sadiq ya tabbatar da afkuwar lamarin inda ya ce binciken da suka fara yi ya nuna mutumin na da taɓin hankali. "Kawo yanzu babu wanda aka kama tunda ba a kan lamarin," in ji shi.

Source: Legit


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN