• Labaran yau


  Mahaifi da ya daure danshi tare da tumaki tsawon shekara 2 a Kebbi ya gurfana a Kotu

  Rundunar yansandan jihar Kebbi ta sanar da gurfanar da wani magidanci mai suna Aliyu Umar a gaban Kotu kisa zargin cin zarafin dansa Jibrin Aliyu bayan ya daure shi tare da Tumaki da kaji a gidansa har tsawon shekara biyu a jihar Kebbi.

  ISYAKU.COM ya labarta maku yadda mahaifin yaron wanda ke zaune a unguwar Badariya a garin Birnin kebbi, ya daure shi bisa zargin lalurar tabin hankali da yaron kefama da shi har tsawo shekara biyu. Duba labarin a nan

  A wata sanarwa ta Shelkwatan yansandan jihar Kebbi ta fitar ranar 12 ga watan Agusta, wanda Kakakin hukumar yansandan jihar Kebbi DSP Nafi'u Abubakar ya sa wa hannu amadadin Kwamishinan yansandan jihar Kebbi, ya sanar cewa hukumar yansanda ta gurfanar da Aliyu Umar a gaban Kotu bisa tuhumar cutar da dansa ta hanyar daure shi tare da Tumaki da Kaji har tsawon shekara biyu.


  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari


  Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Mahaifi da ya daure danshi tare da tumaki tsawon shekara 2 a Kebbi ya gurfana a Kotu Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama