• Labaran yau


  Kotu ta kori karar da yansanda suka shigar kan Sanata Abbo kan marin wata mata

  Wata Kotun Majistare da ke Zuba a babban birnin tarayyar Najeriya ta kori karar da aka shigar kan Sanata Elisha Abbo kan duka da cin zarafin wata mata.

  An ga Sanata Abbo, wanda ke wakiltar Adamawa ta arewa a zauren Majalisar Dattawan Najeriya yana marin wata mata mai suna Osimibibra Warmate. Sakamakon haka yansanda suka gurfanar da shi a gaban Kotu.

  Sai dai Alkalin Kotun, Abdullahi Illela, ya kori karar bisa hurumin cewa masu gabatar da karav sun kasa gamsar da Kotu kan da'awarsu kan kara da suka shigar a kan Sanata Abbo, duk da cewa an ga Sanatan yana marin matar a wani bidiyo, daga bisani kuma aka ga yana ba matar hakuri a wani bidiyo na daban.


  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari


  Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Kotu ta kori karar da yansanda suka shigar kan Sanata Abbo kan marin wata mata Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama