Korarren soja ya yi wa macen yarsanda dan banzan duka tana sanye da kaki a bakin aiki

Rundunar yansandan jihar Lagos ta kama wani  korarren soja mai suna Yemi Ayeni mai shekara 32 bayan ya yi wa macen yarsanda dan karen duka yayin da take gudanar da aiki a kan titi a birnin Lagos mako da ya gabata.

Lamarin ya faru ne a unguwar Shibiri da ke birnin Lagos bayan yarsandan ta tsayar da motar bas da Yemi yake ciki, sakamakon haka Yemi ya harzuka kuma ya kalubalanci yarsanda. Daga bisani lamarin ya rikide ya zama fada.

A wani faifen bidiyo da ya zagaya intanet kamar ruwan dare, an ga yadda Yemi ya dinga dukan wannan hafsar yansanda sanye da Kakin aiki.

Bisa wannan dalili ne bayanai suka nuna cewa Rundunar yansandan jihar Lagos ta kaddamar da bincike kan lamarin har ta kamo Yemi wanda bincike ya nuna cewa ba soja bane kuma ya dade yana addabar jama'a a unguwar Shibiri.


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

Previous Post Next Post

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/H5IqezEzbfJ3YScTo1dk59

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN