Ko shan magani kullum na warkar da ciwon gwiwa, duba abin da ya kamata ka yi

Ciwon gwiwa nau'in amosani gwiwa ciwo ne da ke faruwa musamman ga waɗanda shekarunsu suka miƙa sakamakon zaizayewar gurunguntsin gaɓar gwiwa. Masu wannan ciwo na fama da matsanancin ciwo, wahalar ayyukan yau da kullum da kuma nakasar gaɓar gwiwar idan ciwon ya ta'azzara.


Sai dai, masu fama da irin wannan ciwon gwiwa kan É—auki É—abi'ar shan magungunan ciwon jiki/gaÉ“É“ai kullum. Amma ciwon na ci gaba da dawowa duk lokacin da aikin maganin ya Æ™are. 


Har wa yau, irin waÉ—annan magunguna basu da tasirin warkar da zaizayewar gurunguntsin gwiwa face rage ciwon na wani É—an lokaci. 


Bugu da ƙari, shan magungunan ciwon jiki/gaɓɓai nau'in 'NSAIDs' tsawon lokaci na da haɗarin janyo ciwon gyanbon ciki(olsa) da kuma ciwon ƙoda.


Saboda haka, shan magungunan rage ciwo ba zai magance nakasar gwiwar daga ƙarshe ba. Nakasar gaɓar gwiwa kuwa na iya tsugunar da mutum ko kuma tilasta yin tiyata domin a yi dashen gaɓar gwiwa matuƙar ana son ci gaban aikin gwiwar.


Ɗaukan matakan gaggawa don shawo kan ciwon amosanin gwiwa zai taimaka wajen ceto gwiwar daga nakasa, wanda daga ƙarshe nakasar gwiwar za ta iya tilasta yin dashen gwiwa.


Shan maganin kullum ko kuma tiyatar dashen gwiwa hanyoyi ne da za a iya kauce musu idan aka tintiɓi likitan fisiyo tun ciwon yana matakin farko.


Guji yin fargar jaji game da lafiyarka/ki, tintiɓi likitan fisiyo a yau.


Source: Physio Hausa


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN