• Labaran yau


  Ko me ke kawo tsagar Leɓe? duba dalili da ya sa hakan ke faruwa

  Tsagar leɓe wacce ake cewa "cleft lip" a turance, tawayar haihuwa ce da ake ganinta jifa-jifa a jarirai. Yayin halittar sassan jikin jariri a ciki, ana kammala halittar leɓe ne yayin da ciki ke tsakanin sati huɗu zuwa bakwai.

  Bayan nan, tsagar leɓe kan faru ne idan gefe da gefe na tsokokin leɓe suka gaza haɗewa a tsakiya yadda ya kamata kafin haihuwa. Tsagar leɓe kan kasance a gefe ɗaya na leɓe ko gefe biyun duka, ko kuma a tsakiyar leɓen. Bugu da ƙari, jarirai masu tsagaggen leɓe su kan zo da tsagar ganɗa wacce ake cewa "cleft palate" a turance.

  Sai dai, har i zuwa yanzu, babu wani takamaiman sababin da ke kawo tsagar leɓe ga jarirai. Amma, masana na ganin cewa tsagar leɓe na faruwa ne saboda samun canje-canje ko jirkicewar jigigar halittar jariri wato "genes" a turance.

  Amma ana alaƙanta haɗarin samun tsagar leɓe idan mai juna biyu na da ciwon siga, shan taba sigari, ko kuma amfani da wasu jinsin magungunan farfaɗiya a watannin ukun farko na renon ciki.

  Ana magance tsagar lefe ta hanyar yin tiyata/aiki a leɓe don a haɗe shi. Hakan nan, an fi so a yi tiyatar sa'ad da jariri ke cikin shekarar farko da haihuwa. Saboda haka, da zarar an lura jariri ya zo da tsagaggen leɓe a tuntuɓi likita.

  Source: Physio Hausa


  Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
  https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

  Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
  LATSA NAN

  SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

  Facebook.com/isyakulabari


  Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

  • Facebook Comments
  Item Reviewed: Ko me ke kawo tsagar Leɓe? duba dalili da ya sa hakan ke faruwa Rating: 5 Reviewed By: -
  Koma Sama