Kana jin raɗaɗi, zogi, ko sagewar yatsun hannu?

A yayin da kake jin ciwo, raɗaɗi, zogi, ƙuna, dindiris ko sagewar yatsun hannu alamu ne na yiwuwar kana fama da ciwon nan da ake cewa "Carpal Tunnel Syndrome" a yaren likitanci. Wannan ciwo yana daga cikin ciwukan hannu da suka fi shahara.

Ciwon "Carpal tunnel syndrome" yana faruwa ne a yayin da aka shaƙe, ko aka danne jijiyar laka ta "median nerve" da take kaiwa da komowar saƙonni zuwa yatsun hannu. Wannan jijiyar lakar tana samun matsala ne a dai-dai wani matsatstsen kwararo da ta wuce ta ciki a tsintsiyar hannu da ake cewa "carpal tunnel" a yaren likita.

Wannan hanya ko kwararo da wannan jijiyar laka ta wuce ta ciki yana da bangwayen ƙashi da kuma ƙarfafan jijiyoyin tantani. Saboda da haka, jijiyar ta ratsa ta tsakankaninsu ne.
Wannan ne yasa a yayin da sauran jijiyoyin tantani suka kumbura a kwararon da jijiyar lakar ta bi ake shaƙe ko matse ta.

Wannan jijiyar laka ta "median nerve", ita ce take kai saƙonnin aiki da kuma ji a fatar tafin hannu zuwa yatsun hannu, musamman babban yatsa, manuni, mabiyin manuni da kuma rabin yatsan zobe, sai dai, wannan jijiya ba ita ce ke bai wa rabin yatsan zobe da kuma ɗanƙuri saƙonni ba, wannan yasa matsalar ba ta shafarsu.

Alamomin wannan ciwo sun haɗa da jin:

1. Ciwo
2. Raɗaɗi
3. Zogi
4. Zafi
5. Dindiris
6. Sagewa
7] Da kuma rauni ko kasa iya riƙe wani abu da yatsun ko kuma raunin damƙa. Bugu da ƙari, wannan ciwo ya fi takurawa da daddare.
Waɗanda ke da haɗarin samun wannan ciwo sun haɗa da:
1] Mata masu juna biyu, saboda mata sun ninka maza sau uku wajen samun wannan ciwo.
2] Masu ciwon siga.
3] Ciwon sanyin ƙashi na "Rheumatism"
4] Masu ƙiba
5] Masu sana'o'in da ke buƙatar maimaituwar aikin tsintsiyar hannu ko damƙa akai-akai kamar:
a) Ma'aikatan da ke harhaɗa sassan na'urori ko injina.
b) Masu aiki da injinan yanka ƙarfe ko katako.
c) Matuƙa babura da kekuna.
d) Injiniyoyi da sauran masu gyaran na'urori.
e) Masu sana'ar fenti ko zane-zane.
f) Mabuga rubutu a allon kibod na kwamfuta, da sauransu.

Wannan ciwo ana warkewa a cikin 'yan kwanaki idan aka sami kulawar likitan fisiyo a kan lokaci. Rashin ɗaukar matakin ganin likitan fisiyo da wuri ka iya ta'azzara matsalar har ta kai ga yin tiyata domin a buɗa wa jijiyar lakar hanya.

Idan kana fuskantar alamun wannan ciwo, tuntuɓi likitan fisiyo a yau don fara bankwana da shi.

Source: Physio Hausa


Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

Previous Post Next Post