Mutum 3 sun mutu bayan yan sanda 60 sun sami raunuka sakamakon tarzoma da ta barke domin cin zarfin Manzon Allah da wani ya wallafa a shafinsa na Facebook a birnin Bangalore na kasar India a daren ranar Talata 8 ga watan Agusta.
An kona motoci da dama tare da banka wa gidan dan Majalisa wuta wanda ake zargin dansa ne ya wallafa wannan batanci ga Annabi.
Duk da lallashin jama'a da Dattijai suka yi, haka bai hana tarzoman kazamcewa ba.
Sai dai wanda ake zargi da wallafa batancin, ya ce, ba shi ne ya wallafa wadannan kalamai a Facebook ba. Ya ce wani ya sace ragamarsa ta shiga Facebook kuma ya aikta wannan mugun aiki da sunansa domin ya haddasa wannan rudani a cikin al'umma. Sai dai duk da haka, yansanda sun kama shi domin amsa tambayoyi.
DAGA ISYAKU.COM
https://chat.whatsapp.com/
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/