Yan sandan jihar Kano sun ceto wani bawan Allah mai shekaru 55, Murtala Muhammad da mahaifinsa ya rufe shi a daki bayan daure masa kafa na tsawon shekaru 30.
Jamian yan sanda da yan kungiyar kare hakkin bil adama ta Human Rights Network ne suka ce Muhammad, mazaunin Kofar Fada a karamar hukumar Rogo ta jihar Kano a ranar Alhamis.
An ce an daure shi ne saboda yana fama da tabin hankali kamar yadda Sahara Reotrers ta ruwaito. Muhammad ya ce ya yi farin ciki da aka cece shi daga halin da mahaifinsa ya jefa shi ciki.
Kwamared AA Haruna Ayagi, Shugaban Human Rights Network ya ce tun lokacin Muhammad yana da shekaru 25 a duniya aka rufe shi a gida aka daure kafarsa a jikin reshen itace.
A wani rahoton da Legit.ng ta wallafa, Yan sanda a jihar Kano har ila yau sun ceto wani matashi mai shekaru 32, Ahmad Aliyu, wanda mahaifinsa da kishiyar mahaifiyarsa suka kulle tsawon shekaru bakwai a jihar Kano.
Yan sandan sun kai wannan farmaki ne daren Litinin a Farawa Babban Layi, Mariri Quarters a karamar hukumar Kumbotso ta jihar Kano. Mutumin, wanda hoto da bidiyo suka nuna yana cikin mawuyacin hali ya kwashe kwanaki babu abinci, babu ruwan sha sai dai shan fitsarinsa, HumAngle ta ruwaito.
Wata majiya ta bayyanawa HumAngle cewa mahaifinsa da kishiyar babarsa sun daureshi ne zargin cewa ya fara shaye-shaye da ta'amuni da kwayoyi. Wata mata mai suna Rahama dake zama a Farawa Babban Layi, Mariri Quarters, ta kaiwa yan sanda rahoto a Farawa kuma kungiyar rajin kare hakkin dan Adam suka garzayo cetonsa.
Yayinda yan sanda da yan kungiyar kare hakkin bil adaman suka isa gidan, kishiyar babar ta ce Ahmad ba ya gida, hakan ya sa suka fasa ciki karfi da yaji suka lalubo shi. Tuni yan sanda sun damke mahaifin da kishiyar babarsa kuma aka tafi da Ahmad.
Source: Legit
Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/ JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/ L4xvcwRGM496Eep5J53zXt
Jamian yan sanda da yan kungiyar kare hakkin bil adama ta Human Rights Network ne suka ce Muhammad, mazaunin Kofar Fada a karamar hukumar Rogo ta jihar Kano a ranar Alhamis.
An ce an daure shi ne saboda yana fama da tabin hankali kamar yadda Sahara Reotrers ta ruwaito. Muhammad ya ce ya yi farin ciki da aka cece shi daga halin da mahaifinsa ya jefa shi ciki.
Kwamared AA Haruna Ayagi, Shugaban Human Rights Network ya ce tun lokacin Muhammad yana da shekaru 25 a duniya aka rufe shi a gida aka daure kafarsa a jikin reshen itace.
A wani rahoton da Legit.ng ta wallafa, Yan sanda a jihar Kano har ila yau sun ceto wani matashi mai shekaru 32, Ahmad Aliyu, wanda mahaifinsa da kishiyar mahaifiyarsa suka kulle tsawon shekaru bakwai a jihar Kano.
Yan sandan sun kai wannan farmaki ne daren Litinin a Farawa Babban Layi, Mariri Quarters a karamar hukumar Kumbotso ta jihar Kano. Mutumin, wanda hoto da bidiyo suka nuna yana cikin mawuyacin hali ya kwashe kwanaki babu abinci, babu ruwan sha sai dai shan fitsarinsa, HumAngle ta ruwaito.
Wata majiya ta bayyanawa HumAngle cewa mahaifinsa da kishiyar babarsa sun daureshi ne zargin cewa ya fara shaye-shaye da ta'amuni da kwayoyi. Wata mata mai suna Rahama dake zama a Farawa Babban Layi, Mariri Quarters, ta kaiwa yan sanda rahoto a Farawa kuma kungiyar rajin kare hakkin dan Adam suka garzayo cetonsa.
Yayinda yan sanda da yan kungiyar kare hakkin bil adaman suka isa gidan, kishiyar babar ta ce Ahmad ba ya gida, hakan ya sa suka fasa ciki karfi da yaji suka lalubo shi. Tuni yan sanda sun damke mahaifin da kishiyar babarsa kuma aka tafi da Ahmad.
Source: Legit
DAGA ISYAKU.COM
https://chat.whatsapp.com/
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/