An kwace gawar wani jariri a wajen wata mahaukaciya bayan shafe sama da mako 1 tana yawo da shi a bayanta

Wata mata da aka tabbatar da cewa mahaukaciya ce ta shafe sama da mako daya tana yawo da gawar wani jariri a bayanta, mutane sun gano hakan ne bayan warin gawar jaririn ya fara damunsu.
Matar an ganta a ranar Talata, 18 ga watan Agusta, dauke da gawar yaron a karamar hukumar Effium Ohaukwu dake jihar Ebonyi.
An ruwaito cewa matar ta isa wannan gari ne watanni kadan da suka wuce daga wani wuri da ba a san ko ina bane, inda ta fara zama a wani kangon gida.
Mutane basu san da zamanta a wannan waje ba har sai da mutane suka fara jin wani wari a duk lokacin da ta wuce daga gabansu, sai suka sanar da 'yan sanda bayan an bincika aka gano cewa warin na fitowa daga jikin yaron dake goye a bayanta ne.
Wata majiya ta sanar da jaridar Punch cewa: "Yan sandan sun sanar da wasu cibiyoyi guda biyu dake yankin, cibiyoyin guda biyu sun tara matasa domin kwace jaririn daga hannun mahaukaciyar.
"Sai dai matar taki yadda a kwace jaririn, hakan yasa aka yi ta fama da ita. Sai da matasan suka yi mata wayo sannan suka samu suka kwace gawar jaririn.
"Gawar yaron tuni har ta fara rubewa a bayanta, saboda tana goye da shi fiye da mako daya. Matasan sun kwace gawar daga wajenta inda suka binne shi a makabarta a ranar Talata."
Agbo Sunday ya tabbatarwa da jaridar Punch cewa an binne gawar jaririn a ranar Talata kuma tuni mutane sun cigaba da harkokinsu kamar yadda suka saba a baya.
"Mutane su koma su cigaba da kasuwancin su, saboda komai ya wuce an dauki mataki akan lamarin. An binne gawar jaririn a ranar Talata,"cewar shi.
Source: Legit

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

إرسال تعليق

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

أحدث أقدم

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN