Amfanin atisaye ga mai juna biyu.

Sashin lura da lafiyar mata na likitancin fisiyo na da muhimmancin gaske ga masu juna biyu. Saboda bincike ya nuna cewa masu juna biyun da suka halarci ajujuwan ɗaukar atisaye yayin rainon ciki na samun garkuwa daga wasu matsalolin rainon ciki da haihuwa kamar haka:
 
1. Magance matsanancin ciwon baya da ƙugu.
2. Rage haɗarin kamuwa da ciwon siga yayin rainon ciki.
3. Rage haɗarin kamuwa da hawan jini yayin rainon ciki, wanda alama ce daga cikin alamun da ke nuni da haɗarin samun jijjiga.
4. Bunƙasa aikin tsokokin ƙugu da ke temaka wa uwa yayin naƙuda, domin haihuwa cikin sauƙi. Bunƙasa aikin waɗannan tsokoki zai rage haɗarin kasa haihuwa da kai; wanda ka iya tilasta yin tiyata/aiki domin ciro jariri.
5. Rage haɗarin samun matsalar ƙwacewar fitsara, ko kuma yayyon fitsari.
6. Rage haɗarin buɗewar ƙugu - matsala ce da ƙasusuwan ƙugu kan buɗe fiye da kima saboda raunata tantanan da ke riƙe da ƙasusuwan ƙugu yayin naƙuda.
7. Magance matsalar kumburin ƙafa, tafin sawu.
8. Magance matsalar ƙwacewar fitsari yayin da kuma bayan haihuwa.
9. Raga samun ƙiba/ teɓa fiye da ƙima yayin da kuma bayan haihuwa.
10. Rage damuwa / yawan bacin rai.
11. Rage haɗarin haihuwar bakwaini da dai sauransu.
 
Sai dai, atisaye yayin rainon ciki na buƙatar tantance mai juna biyu kafin ta fara atisaye. Saboda haka, zai fi kyau a yi atisaye ƙarƙashin kulawar likitan fisiyo domin wanyewa lafiya.
 
Tuntuɓi likitan fisiyo a dukkan asibitocin da ke da sashin fisiyo (physiotheray) domin fara ɗaukar atisayen rainon cikin domin samun alfanun da aka ambata. 
 
Source: Physio Hausa
 

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

Previous Post Next Post

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

https://chat.whatsapp.com/H5IqezEzbfJ3YScTo1dk59

Domin zama wakilinmu a garinku LATSA NAN

Korafi ko aiko labari LATSA NAN