Alamomin ciwon hanta, matakan kariya da abin da ya kamata ka sani game da cutar

Hukumar Lafiya ta Duniya ce ta ware duk ranar 28 ga watan Yulin kowace shekara don bikin ranar hanta ta duniya. Ana gudanar da bikin duk shekara ne da zimmar shirya gangamin wayar da kai kan ciwon hanta, samo nagartattun matakan kariya, da ma samar da hanyoyin tallafa wa miliyoyin masu fama da ciwon hantar a faÉ—in duniya.

Taken ranar na bana shi ne yin rayuwa "nan gaba da babu ciwon hanta" ciki.

Ciwon hanta wanda ake cewa 'viral hepatitis' a turancin likita, ciwo ne da ke kama hanta bayan harɓin ƙwayoyin cutar bairos ga hanta. Wannan ciwon hanta, ciwo ne da ke haddasa kumburin hanta, wanda ke janyo matsalolin lafiya har da daji / kansar hanta.

Ƙwayoyin cutar na yaɗuwa ne ta hanyar haɗuwar jini, ruwan mani yayin saduwa da sauran ruwayen jiki daga mai ɗauke da ciwon hantar zuwa wanda ba ya ɗauke da ciwon.

Akwai nau'o'in ƙwayar bairos biyar da ke kama hanta kamar haka: A, B, C, D da kuma E. Sai dai, nau'o'in B da C sune suka fi lashe rayuka, inda suke lashe rayuka miliyan 1.3 duk shekara.

Bugu da ƙari, Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce kimanin mutum miliyan 325 ke fama da ciwon hanta nau'in B da C a duniya. A yayin da ciwon hanta nau'in B kawai ke lashe rayuka 900,000 duk shekara.
Har wa yau, hukumar lafiyar ta ce, kaso 10 cikin 100 ne kawai na masu fama da cutar hanta nau'in B da kuma kaso 19 cikin 100 na masu fama da ciwon hanta nau'in C suka san suna É—auke da cutar.

Wannan na nuni da miliyoyin mutunen da ke fama da ciwon hantar amma basu sani ba, kuma hakan na faruwa ne saboda ƙarancin zuwa asibiti domin gwajin ciwon hanta akai-akai.

Haka nan, kaso 42 cikin 100 ne kawai na yaran da ake haifa a faÉ—in duniya suke iya samun allurar rigakafin ciwon hanta nau'in B bayan haihuwarsu. Saboda haka hukumar ke sake jaddada kira game da yaÉ—uwar cutar daga uwa zuwa jariri cewa, ya kamata dukkan jarirai su sami rigakafin ciwon hanta nau'in B bayan haihuwarsu.

Daga cikin alamun ciwon hanta akwai:

1] Bayyanar kalar rawaya a ido ko fata (shawara).
2] Zazzaɓi
3] Tashin zuciya.
4] ÆŠaukewar sha'awar abinci, da sauransu.

Wasu daga cikin matakan kariya sun haÉ—a da:
 
1. Tattaunawa da likita kan É—aukar alluran rigakafin ciwon hantar.
2. Kada a yi amfani da allura, reza ko burushin goge baki da wani yake amfani da su.
3. Ga masu juna biyu, tattauna da likita kan yadda za a kare yaÉ—uwar cutar zuwa jariri.
4. A yi amfani kaɗai da abubuwan yanka jiki (kamar askar aski ko askar tiyatar likita) da aka tsabtace su daga dukkan ƙwayoyin cuta.
5. A lizimci amfani da kwaroron roba(condom) ko da yaushe yayin saduwa da wanda ke É—auke da cutar ko haÉ—arin kamuwa da cutar.
6. Idan mai yiwu wa ne, zaɓi shan ƙwayar magani maimakon yin allura.

Haka nan, kana cikin haÉ—arin kamuwa da ciwon hanta:

1] Idan an taɓa yi maka aiki/tiyata a jiki ko a haƙori da kayan aikin da ba a tabbatar da an tsabtace su daga dukkan ƙwayayyakin cuta ba.
2] Idan an taɓa ƙara maka jinin da ba ai masa gwajin cutar hantar ba. Kuma aka tabbatar babu cutar.
3] Idan mahaifiya na É—auke da cutar yayin da aka haife ka.
4] Idan kana ɗauke da cutar ƙanjamau ko cuta mai karya garkuwar jiki.
5] Idan an yi maka allura da allurar ko sirinjin da aka yi wa wani allura da ita.
6] Idan kana cin abincin ko abinsha da ya lalace ko mara tsabta.

Tabbatar an yi maka gwajin ciwon hanta domin sanin matsayinka a yau!

Source: Physio Hausa

Latsa nan ka shiga group din mu domin samun Labaran mu ta Whatsapp
https://chat.whatsapp.com/JKBP5KgalYg3iQRBQoFVAE

Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN

SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA

Facebook.com/isyakulabari


Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/L4xvcwRGM496Eep5J53zXt

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN