A ranar Asabar, 8 ga watan Agusta ne aka sanar da mutuwar sanata mai wakiltan Ogun ta gabas, Buruji Kashamu, bayan ya yi fama da cutar korona.
Sanata Murray Bruce ne ya sanar da mutuwar sanatan a shafinsa na Twitter.
Ga wasu ‘yan abubuwa da baku sani ba game da marigayi dan siyasan.
1. An haifi Kashamu a jihar Ogun, a ranar 19 ga watan Mayu 1958.
2. Ya fara karatunsa a makarantar firamare na Ansarudeen, Ijebu Igbo sannan ya bar makarantar a 1972 inda ya kammala karatunsa na firamare a St. John Modern School, Lagos.
3. Kashamu ya kuma halarci makarantar yamma a kwalejin Igbobi yayinda yake aiki a matsayin jami’in lasisi.
4. Daga bisani ya je Landan inda ya yi darusa a fannin kasuwanci a Kwalejin Pitman, Landan.
5. An karrama Kashamu da digiri na uku a jami’ar Cambridge Graduate University, da ke Massachusetts, a wani kasaitaccen taro da aka shirya a Lagas.
6. Ya kasance jigo a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Ogun.
7. Ya tsaya takara kujerar sanatan Ogun ta gabas sannan ya kayar da abokin adawarsa da kuri’u 99,540.
8. An nada dan siyasan a matsayin shugaban kwamitin gudanarwa na PDP a yankin kudu maso yammacin Najeriya.
9. A 2018, an dakatar dashi daga jam’iyyar Peoples Democratic Party, hukuncin da wata kotun Abuja ta soke a watan Oktoba 2018.
Source: Legit
DAGA ISYAKU.COM
https://chat.whatsapp.com/
Domin aiko labari, shawara ko tuntubarmu
LATSA NAN
SHAFUKANMU NA SADA ZUMUNTA
Facebook.com/isyakulabari
Domin samun sassauka, ingattacciya kuma kwakkwarar DATA ta MTN, latsa nan https://chat.whatsapp.com/